Na saci Baibul ne don in karanta in kuma yaɗa kalmar Ubangiji, wanda ake zargi ya fada wa kotu

Na saci Baibul ne don in karanta in kuma yaɗa kalmar Ubangiji, wanda ake zargi ya fada wa kotu

  • Wani mutum mai shekaru 30 a kasar Kenya da aka gurfanar a kotu bisa satar Baibul mai tsarki guda biyu ya bawa kotu amsa mai ban mamaki
  • Augustine Wanyonyi, ya yi ikirarin cewa ya saci Baibul din ne domin ya tafi ya rika karantawa, ya fahimci sakon da ke ciki ya kuma rika yin wa'azi a maimakon halaka kansa
  • An kama Wanyonyi ne bayan na'uarar daukan bidiyo ta CCTV a shago ta nuna cewa ya saka Baibul biyu a kamfensa ya fita ba tare da biyan kudi ba

Kenya - Wani mutum da aka kama saboda laifin satar littafin Baibul mai tsarki har guda biyu ya bada uzuri mai ban mamaki bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Yayin da aka gurfanar da shi gaban Mai shari'a Susan Shitubi, wanda ake zargi mai suna Augustine Wanyonyi ya yi ikirarin cewa ya sace Baibul din ne domin ya rika karantawa ya kara sanin Ubangiji, rahoton BBC Hausa.

Kara karanta wannan

'Allah baya tare da kai': Wani mutum ya faɗa wa Fafaroma a cikin taron mutane

Na saci Baibul ne don in karanta in kuma yaɗa kalmar Ubangiji, wanda ake zargi ya fada wa kotu
Na saci Baibul ne don yaɗa kalmar Ubangiji, wanda ake zargi ya fada wa kotu. Hoto: LIB
Asali: Twitter

Da ya ke jawabi bayan mai gabatar da kara ta karanto rahoton yan sanda da ke nuna Wanyonyi ya tafi shagon Naivas a kan titin Moi Avenue a Nairabi misalin karfe 3 na ranar Litinin, 30 ga watan Janairu ya sace Baibul biyu ya boye a kamfensa, wanda ake zargin ya ce ya yi imanin littafin Allah zai shirya shi.

Yadda aka gano ya yi satar

An gano shi ne a hanyar amfani da na'urar daukan bidiyo na CCTV da ke shagon inda ta nuna bai biya kudin ba ya tafi.

A cewar rahoton kotu, mutumin mai shekaru 30 ya yi ikirarin cewa ya fara tunanin halaka kansa ne bayan an rushe gidansa a Mukuru Kwa Njenga.

Da aka tambaye shi mai yasa ya saci har guda biyu da kudinsa ya kai Ksh2,100, wanda ake zargin ya ce yana son ya bawa matarsa daya shi kuma ya rika karanta guda daya, rahoton LIB.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023

Wanyonyi ya ce;

"Na saci Baibul don in rika karantawa, in fahimta abinda ke ciki sannan in rika yada kalmar Ubangiji a maimakon kashe kaina saboda matsalolin da na ke fuskanta."

Mai shigar da karar ta shaida wa kotu cewa wannan ba shine karon farko da ake tuhumar wanda ake zargin da sata a shago ba, an taba tuhumarsa a Disambar 2021.

Alkalin kotun ta ce a shirya takardun yanke masa hukunci cikin kwana 7, zai sake gurfana a kotu a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani labarin, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Somefun ya yanke wa Alaka watanni 3 a gidan yari ko kuma ya bayar da tarar N100,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164