Da Dumi-Dumi: An jiyo ƙarar harbe-harben bindiga kusa da fadar shugaban ƙasar Guinea
1 - tsawon mintuna
Guinea - Rahoton da muke samu na nuna cewa an jiyo ƙarar harbe-harbe na tashi a kusa da fadar shugaban ƙasa dake Guinea, babban birnin ƙasar Guine-Bissau ranar Talata.
The Cable ta tattaro cewa duk da har yanzun ba'a gano musabbabin harbe-harben ba, amma Dakarun sojojin ƙasar sun zagaye fadar yayin da shugaban ƙasa, Umaro Sissoco Embaló, ke gudanar da taro da yan majalisar zartarwansa.
Tun bayan da ƙasar ta samu yancin kai daga ƙasar Portugal a 1974, Guinea-Bissau ta sha fama da juyin mulki kala daban-daban, tawayen sojoji da kuma yi wa yan siyasa kisan gilla.
Ƙarin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng