Sunaye Da Hotuna: Bakaken Fata 5 Da Suka Fi Kudi a Duniya
A cikin sunayen biloniyoyin duniya na jaridar Forbes, akwai biloniyoyi 2,775 a duniya kuma fiye da 10 daga cikinsu bakaken fata ne.
Rahoton nan ya jero mutane 5 na masu kudin duniya wadanda duk bakaken fata ne, har ila yau har da sana’o’in da suke yi da suka kawo musu dukiyoyin da suka mallaka, rahoton Daily Trust.
1. Aliko Dangote
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Aliko Dangote, shi ne mutumin da yafi kowa kudi a Najeriya kuma dan kasuwa ne, mai taimakon al’umma kuma shi ne shugaba kuma mai kamfanin Dangote Group.
A watan Janairun 2022, an kirga yawan dukiyarsa ta kai dala biliyan 10.6. Ya kafa kamfaninsa na Dangote Group a shekarar 1977 wanda har yanzu kasuwancin nasa ya ke ta bunkasa zuwa tiriliyoyin nairori.
Kamfanin nasa ya na samar da kayan abinci, siminti da sauran abubuwa na masarufi. Kamfanin ya na samar da gishiri da siga kuma yanzu haka ya na aiki tukuru wurin samar da matatar man fetur wacce ta fi ko wacce a nahiyar Afirka.
2. Mike Adenuga
Mike Adenuga shi ne na biyu a masu kudin Afirka kuma na biyu a attajiran Najeriya. Shi ne mai kamfanin Globacom, wanda kamfani ne na sadarwa na biyu a Najeriya kuma yanzu haka ya na aiki har a kasar Ghana da jamhuriyar Benin.
A watan Janairun 2022, yana da dukiya mai yawan dala biliyan 9.1. Yana da kaso a Equitorial Trust Bank da kuma kamfanin man fetur na Conoil. Yanzu haka akwai mutane miliyan 55 masu amfani da Globacom a duniya yayin da Conoil ta ke da rijiyoyin mai 6 da take aiki da su.
3. Robert F. Smith
Robert F. Smith ma’aikacin banki ne, injiniyan sinadarai sannan kuma dan kasuwar Amurka ne. Shi ne mai kamfani kuma shugaban Vista Equity Partners, har ila yau shi ne mutum na 480 a cikin jerin biloniyoyin duniya da jerin Forbes ya gabatar a shekarar 2018. A watan Janairun 2022 dukiyarsa ta kai dala biliyan 5.
A shekarar 2017, shi ne mutum na 100 a cikin hamshakan ‘yan kasuwan duniya da Forbes ta jero. A shekarar 2019, lokacin bayar da lambar yabo ta Pitchbook Private Equity, an ba shi jinjinar ‘Executive of the year.’
Har ila yau shi ne ya zama mafi arzikin dan Afirka kuma mazaunin Amurka na shekarar 2018 bayan ya zarce Oprah Winfrey arziki.
Ya yi aiki da Air Products & Chemicals, Goodyear Tire ane Rubber Company sannan ya yi aiki da Kraft General Foods a matsayin injiniyan sinadarai.
4. David Steward
David Steward dan kasuwa ne na Amurka, kuma shi ne shugaba kuma mai kamfanin World Wide Technology, daya daga cikin manyan harkokin kasuwanci na nahiyar Afirka da Amurka da ke hada-hada a Amurka.
Sannan yana daya daga cikin biloniyoyi 4 da ke Amurka kuma shi ne na 745 a jerin biloniyoyin shekarar 2019 da Forbes ta lissafo.
A watan Janairun 2022, ya na da kudi kimar dala biliyan 3.9 inda kamfaninsa ya kai kimar dala biliyan 12. Ya na da manyan abokan ciniki kamar Verizon, Citi Bank da sauran su.
5. Oprah Winfrey
Oprah Winfrey ce kadai mace a cikin jerin bakaken fata masu arziki na duniya, kuma ta na gabatar da shiri, furodusa ce ta shirin gidan talabijin, jarumar fina-finai, marubuciya kuma mai taimakon al’umma.
Ta yi fice ne da wani shirin ta na gidan talabijin na ‘The Oprah Winfrey Show’, wanda ake shirya shi daga Chicago. Shirin ta shi ne mafi daukaka a cikin shirye-shiryen gidan talabijin a tarihi.
Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi
A watan Janairun 2022 Oprah Winfrey tana da dukiya mai yawan dala biliyan 2.7. Tun shekarar 1986 har zuwa 2011 ta ke yin shirin tsawon shekaru 25 kenan.
Ita ce bakar fata ta farko a arewacin Amurka da ta zama biloniya. Kuma ta zama mace ta farko mafi daukaka a duniya a shekarar 2007.
Ta hada shirya labarai tun tana da shekara 19 a duniya kuma ta yi suna kwarai da shirye-shiryen ta na talabijin.
Asali: Legit.ng