An sake nada ‘Yar Najeriya, Amina Mohammed a kujerar Majalisar dinkin Duniya a karo na 2
- António Guterres ya zabi Amina J. Mohammed ta zarce a kujerar sakatariyar mataimakiyar UN
- Da take magana a shafinta na Twitter, Miss Amina J. Mohammed ta tabbatar da cewa ta karbi mukamin
- Amina J. Mohammed ‘Yar asalin Najeriya ce da take rike da kujerar mataimakin shugaban majalisar UN
United States - Shugaban majalisar dinkin Duniya, Mr. António Guterres ya bada sanarwar sake nada Ms. Amina J. Mohammed a matsayin mataimakiyarsa.
A wata sanarwa da ta fito daga majalisar dinkin Duniya, an ji cewa António Guterres ya zabi Amina J. Mohammed ta cigaba da rike kujerar da ta ke a kai.
Guterres ya yabi Mohammed, yace ta kawo sauye-sauyen da ba a taba gani ba a tarihin majalisar.
Daga cikin kokarin da tsohuwar Ministar Najeriyar tayi akwai tabbatar da cewa kasashen da ke karkashin UN sun dabbaka manufofin SDG da aka shigo da su.
A shekaru biyar da suka wuce, an ga yadda kasashen Duniya suka rungumi kadarorin SDG da nufin kawo cigaba a fadin Duniya da inganta rayuwar mutane.
Amina Mohammed ta taka rawar gani wajen yakar matsalolin sauyin-yanayi, sannan kuma ta bada gudumuwa wajen tsare yarjejeniyar nan ta Paris Agreement.
Jaridar nan ta Premium Times ta ce António Guterres ya jinjinawa mataimakiyar ta sa a kan kokarin da tayi wajen rage radadin tasirin annobar cutar COVID-19.
Na ji, na karba - Amina Mohammed
Da take bayani a shafinta na Twitter, Ms Mohammed ta karbi wannan mukami da aka sake ba ta.
“Ina mai kankan da kai da karbar wa’adi na biyu a matsayin mataimakiyar sakatariyar UN tare da @antonioguterres.”
“Zan fara wannan aiki da alfaharin zama mace ‘Yar Najeriya da nufin cika alkawuran SDG. Za mu tafi tare da kowa.”
- @AminaJMohammed
Daga ina Mohammed ta zo UN?
Rahoton ya ce idan za a tuna Amina Mohammed ta rike Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari kafin ta zama mataimakiyar sakatariyar majalisar UN a 2017.
Mutumiyar Najeriyar tayi aiki da tsohon shugaban majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-moon a matsayin hadimarsa bayan tayi aikace-aikace da gwamnatin Najeriya.
Najeriya tayi rashi
Rahotanni sun ce tsohon shugaban kasa a Najeriya, Cif Ernest Shonekan ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayi Ernest Shonekan ya rike mulki na ‘yan kwanaki kadan a Najeriya. Cif Shonekan bai dade a kan mulki ba sai Janar Sani Abacha ya yi masa juyin-mulki.
Asali: Legit.ng