Shugaban Koriya ta arewa ya haramta dariya na tsawon kwana 11 a ƙasar
- Shugaban kasar Koriya ta arewa ya haramta wa 'yan kasar dariya ko nuna wata alamar farin ciki na tsawon kwana 11 a dukkan fadin kasar
- Wannan lamarin na zuwa ne domin makokin cikar mahaifinsa shekaru 10 da rasuwa wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 17
- An umarci 'yan sanda da su hana jama'a nuna alamar farin ciki kama daga shan giya, a ranar 17 ga wata kuwa, har cefane an haramta zuwa yin shi
- A cikin kwanakin, ko da kuwa mutuwa aka yi a kowanne gida, ba a yarda a yi kuka mai sauti ba kuma ba za a fitar da gawar ba sai bayan cikar makokin
Koriya ta arewa - Shugaban kasar Koriya ta arewa, Kim Jong-un ya haramta wa 'yan kasar sa nuna kowacce irin al'amari farin ciki na tsawon kwanaki 11 domin cikar shekaru 10 da rasuwar Kim Jong-Il.
Kamar yadda rahotannin The Telegraph suka bayyana, wannan alamun nuna farin cikin sun haramta a bayyana su kama daga dariya ko shan giya na tsawon kwanaki 11 domin makoki.
A ranar 17 ga watan Disamba kuwa, wacce ita ce ranar da Kim Jong-Il ya rasu, an haramta wa kowa zuwa cefane, Tribune Online ta ruwaito.
"A yayin makokin, dole ne ba za mu sha giya ba, dariya ko kuma wasu al'amuran nishadi," Wani shugaba a kasar daga birnin Sinuiju da ke iyakar arewa maso gabashin kasar ya sanar a Radio Free Asia (RFA).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ko da kuwa iyalin ka sun mutu a yayin makokin, ba a yarda ka yi kuka mai sauti ba kuma ba za a fitar da gawar ba har sai an kammala makokin. Ba a amince jama'a su yi murnar ranar zagayowar haihuwarsu ba idan ta fada cikin kwanakin makokin."
Kim Jong-il, wanda ya mulki masarautar daga 1994 har zuwa mutuwarsa a 2011 bayan kamuwa da ciwon zuciya a shekaru 69 da yayi a duniya, shi ne mahaifin shugaban kasar na yanzu, Kim Jong-un.
A zamanin mulkinsa ne aka fuskanci wani babban ibtila'i a kasar Koriya ta arewa, wata gagarumar yunwa da aka yi a shekarun tsakiyar 1990s wanda ake kira da 'Arduous March'. Kiyasi ya nuna cewa, rayuka 3.5 miliyan ne suka salwanta a cikin shekaru hudu kacal.
Kim Jong-II ya mulki kasar Koriya ta arewa na tsawon shekara 17 kafin mutuwarsa a shekarar 2011.
A kowacce shekara ake yin makokin mutuwar Kim Jong-II da mahaifinsa Kim II-sung a kasar. A kowacce shekara kuwa na tsawon kwanaki goma ake makokin amma an kara shekara daya ne wannan karon saboda cikarsu shekaru goma tun bayan mutuwar Kim Jong-II.
"A baya mutanen duk da aka kama suna shan giya a yayin makokin ana kama su sannan a yi musu hukunci kamar 'yan ta'adda. Ana dauke su kuma ba a sake ganinsu har abada," majiyar tace.
An ja kunnen 'yan sanda da su nemo duk wadanda basu nuna matukar fushinsu ba kamar yadda RFA tace kamar yadda wani shugaba daga yankin Hwanghae ya sanar.
"Daga ranar farko ta watan Disamba, za su fara aiki na musamman domin dakile duk wasu al'amura da za su hana mutane makokin," majiya ta biyu ta sanar yayin da ta bukaci a boye sunanta.
"Wata daya 'yan sandan ke dauka suna aiki, na ji labarin cewa ba a amince wa jami'an tsaro su yi bacci ba kwata-kwata."
A wannan lokacin, ana bukatar 'yan Koriya ta arewa da su yi kokarin ciyar da talakawa da masu neman abin ci.
A halin yanzu, kasar Koriya ta arewa na fama da rashin abinci sakamakon annobar korona da aka yi, lamarin da yasa ake tsoron aukuwar Arduous March karo na biyu.
Shugaban Koriya ta Arewa ya haramtawa 'yan ƙasarsa saka irin tufafinsa, ya hana shaguna sayar da irin tufafin
A wani labari na daban, shugaban Koriya ta arewa, Kim Jong-Un ya haramta wa duk wasu ‘yan kasar kwaikwayon irin salon sutturar da ya ke saka wa.
Shugaban da gaske ya ke don ya umarci ‘yan sanda da yawata cikin kasar don kwace irin rigunan sanyinsa daga jama’a da masu shagunan da ke siyarwa.
Radio Free Asia sun ruwaito yadda aka haramta amfani da rigar sanyi ta fatar dabbobi don gudun kwafar salo irin na babban shugaban.
Asali: Legit.ng