A karon farko, wani yayi amfani da goran ruwa ya gina otel mai yawa kan teku, ana biyan N40,000 don kwana ciki
- Wani mutum ya yi amfani da fasaha ta musamman wurin mayar da bola dukiya ta hanyar amfani da gorunan roba wurin gina Otal mai yawo a saman ruwa
- Eric, mai fasahar ta musamman ya tara gorunan roba guda 800,000 da ya tattara su sannan ya kera otal din a bakin teku ta wurin Ivory Coast
- A otal din nasa mai yawo saman ruwa akwai abubuwan birgewa kamar WiFi da na’urar sanyaya wuri inda kwastomomi ke biyansa N40,000 duk kwana daya
Mutane da dama su na ganin gorunan roba da aka yi amfani da su a matsayin bola, amma wani mutum mai dabara, Eric ya kallesu a matsayin kayan gine-gine kuma sai da ya tabbatar da fasahar tasa.
Mutumin wanda ya yi hijira daga Ivory Coast zuwa Afirka ya gina otal na farko wanda ya ke yawo a saman ruwa bayan ya yi amfani da gorunan roba dubu dari takwas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yanzu haka yana amfani da otal din a matsayin hanyar samun kudi
Otal din mai yawo a saman ruwa ya zama hanyar samun kudin Eric inda ya ke samun baki a kalla guda 100 a duk mako.
Otal ne mai matukar kayatarwa don ya na da WiFi, hasken rana da kuma na’urar sanyaya wuri. Bisa bukatar bakin, za a iya matsar da otal din daga wuri zuwa wuri a saman ruwa.
Eric ya bukaci kara gina wasu otal din masu tafiya a kan ruwa
Bayan ganin tarin nasarorin da ya samu a matsayinsa na mutum na farko da ya kera irin wannan otal din, dan kasuwar ya bukaci a kara gina irinshi.
Har ila yau ya nemi a tara masa gorunan roba wadanda ake zubarwa don a amfana da su maimakon a zubar a shara.
Ya bukaci taimakon yara wurin tattaro masa gorunan roba don su na saukin samo su, musamman kusa da Ivory Coast.
An hada otal din da robobi amma har da katako aka yi amfani. An samu bidiyon otal din ne bayan Nas Daily ta wallafa a shafinta na Facebook.
Mutane daga kafafen sada zumunta sun yita yaba wa fasahar
Sadia Noor ta ce:
“Babbar jinjina gareka Eric.
“Ka yi aiki mai kyau ta hanyar amfani da robobin da ake zubarwa wurin gina otal. Ana yin abu mai amfani cikin abubuwa marasa amfani, wannan sako ne a garemu.”
Margarita Kefalaki ya ce:
“Fasahar mai birgewa ko kuma ta shirme? Da bola aka hada otal mai yawo saman ruwa, shiritattun mutane da fasaharsu. Mun gode da ka fargar da mu.”
Christina Sayson Chaneco-mejia ta rubuta:
“A gyara duniyar don ta inganta ta zama wuri mai dadi ga mutanen da ke rayuwa cikinta. Gaskiya ka yi tunani mai kyau, ina yaba maka.”
Fayola Williams kuwa ya ce:
“Wannan tunani ne mai kyau. More rayuwa tare da barin wani abu da za a tuna da kai. Tunanin mutumin nan ya birge ni.”
Asali: Legit.ng