Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar COVID-19
- Bill Gates ya na ganin COVID-19 ta gama kamarin da za tayi, sai dai abin ya lafa a shekarar 2022
- Dattijon da ya kafa kamfanin Microsoft ya fitar da wasika, ya na cewa an shiryawa Coronavirus
- Ba’Amurken ya yaba da yadda aka kirkiro magunguna, amma yace babu adalci wajen yadda ake rabon
United States - Attajiri kuma babban ‘dan kasuwan nan, Bill Gates, yace Duniya ta shirya yadda za ta yaki sababbin nau’ukan cutar COVID-19 irinsu Omicron.
Jaridar Bloomberg tace hakan ya na zuwa ne bayan hukumar lafiya ta Duniya watau WHO, ta nuna damuwar ta a kan hadarin samfurin kwayar Omicron.
A wata wasikar karshen shekara da ya rubuta, Mista Bill Gates yace hakika bullowar Omicron abin damuwa ne, amma yace masana su na aikin bincike a kai.
Yace tun da aka fara wannan annoba, ba ayi lokacin da aka yi kyakkyawan tanadi irin yanzu ba.
“Abin da mu ka sani shi ne: A yanzu Duniya ta shirya tsaf domin ta magance samfurori (na cutar COVID-19) masu yiwuwar yin illa.”
“Ina sa ran an zo karshen lamarin. Akwai wauta inda aka yi wani hasashe, amma ina tunanin cutar za ta lafa a cikin 2022.” – Bill Gates.

Asali: UGC
Gates yace an yi nisa matuka wajen samar da magunguna, ya kuma kara da cewa ba a taba fito da magani aka yada shi a kasashe kamar lokacin annobar nan ba.
Inda matsalar ta ke - Gates
Sai dai Attajirin mai shekara 65 a Duniya ya koka a kan matsalar da ake samu wajen yada magunguna da yadda wasu samfurori suke cigaba da bayyana.

Kara karanta wannan
Yadda mu ka yi da Tinubu a gidansa – Shekarau ya yi magana a game da silar rikicin APC a Kano
Business Insider ta rahoto Bill Gates yana cewa kokarin da aka yi na samar da magunguna (ba daya ba) a shekarar da cutar ta karade Duniya, ikon Ubangiji ne.
A wasikar ta shi, Gates yace abin da ya ci masa tuwo a kwarya shi ne rashin adalci wajen raba magungunan cutar, yace ya kamata a fara alluran ne da tsofaffi.
Omicron ta shigo gari
Idan za a tuna, a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2021, hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasar Afrika ta kudu (NICD) tace an gano sabon samfurin COVID-19.
Wannan samfuri na B.1.1.529 wanda daga baya aka yi wa lakabi da Omricon, shi ne ‘dan auta a gidan cutar murar mashako ta Coronavirus da ta bayyana a 2019.
Asali: Legit.ng