An yanke wa wani hukuncin kisa saboda fim ɗin 'Squid Game' a Korea ta Arewa
- An yanke wa wani mutum hukuncin kisa a kasar Korea ta Arewa saboda smogal din fim din 'Squid Game' da ya yi fice a yanzu
- Mutumin ya yi dabara ne ya shiga da fim din cikin kasar a cikin na'urar ajiye bayanai ta USB drive sannan ya raba wa yan makaranta
- Yan makaranta su bakwai suma an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar da hukunci mai tsanani
Korea ta Kudu - An yanke wa wani mutum dan kasar North Korea hukuncin kisa saboda yin smogal din fim din 'Squid Game' zuwa cikin kasar.
A cewar Radio Free Asia, an kama mutumin da ba a bayyana sunansa ba yana raba wa mutane fim din na kasar Korea ta Kudu.
An gano cewa ya shigo da fim din cikin kasar a boye ne cikin na'urar USB drive daga China.
An kuma kama daliban sakandare su bakwai suna kallon fim din mai dogon zango, daya daga cikinsu an yanke masa hukuncin daurin rai-dai-rai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran daliban biyar kuma an yanke musu hukuncin daurin shekaru biyar-biyar da horaswa mai tsanani yayin da wasu malamansu sun rasa aikinsu wasu kuma an tura su aiki a kauyuka.
Majiyoyi da suke da kusanci da lamarin sun ce za a zartar wa mutumin hukuncin kisar ne ta hanyar harbe shi, The Cable ta ruwaito.
RFA ta ce wannan shine karo na farko da Korea ta Arewa ke hukunta yara masu kananan shekaru 'a yunkurin hana su koyi da dabi'un wasu kasashe da kabilu.
Wata majiya daga jami'an tsaro ta ce:
"Jami'an da ke sa ido kan masu kallon fina-finan da aka haramta ne masu suna 109 Sangmu suka kama su bayan an tsegunta musu.
"Lamarin ya fara ne kimanin mako guda da ya wuce yayin da dalibin sakandare ya siya USB drive dauke da fim din Korea ta Kudu na Squid Game ya kalla tare da wani abokinsa na kusa.
"Daga nan suka fada wa sauran abokansu dalibai, wadanda suka nuna sha'awar son kallon fim din kuma suka basu USB drive din."
Me fim din 'Squid Game' ya kunsa?
Fim din na 'Squid Game' labari ne inda aka tattaro mutane 456 daga cikin al'umma da suke fama da bashi aka bukaci su yi wasanni irin na kananan yara.
Wanda ya yi nasara a karshe zai lashe kyautar ₩45.6 biliyan amma wadanda ba su yi nasara ba mutuwa za su yi.
Tun bayan sakinsa, 'Squid Game' ya shiga jerin fina-finan Netflix mafi fice da samun karbuwa wurin masu kallo.
Rahotanni sun yi ikirarin cewa fim din ya yi kamanceceniya da yadda ake rayuwa a North Korea ne inda ake gwara talakawa da junansu ta hanyar ba su ayyuka masu hadari ga kuma rashin tabbas.
Asali: Legit.ng