Bidiyon yadda aka tsinka wa sabon gwamna mari yayin da yake jawabin rantsarwa

Bidiyon yadda aka tsinka wa sabon gwamna mari yayin da yake jawabin rantsarwa

  • Wani fusataccen mutum ya tsinka wa sabon gwamnan Iran mari yayin da ake bikin rantsar da shi
  • Kamar yadda bidiyon ya bayyana, Gwamna Birgediya Janar Abedin Khorram, ya na kan mumbari yayin da mutumin ya falla masa mari
  • Da gaggawa jami'an tsaron farin kaya suka hanzarta kai wa gwamnan dauki, duk da har yanzu ba a san dalilin marin ba

Iran - Wani fusattaccen bawan Allah ya falla wa sabon gwamnan yankin arewa maso yamma na Iran mari ana tsaka da rantsar da shi a ranar Asabar da ta gabata.

Farmakin da aka kai wa gwamnan a yankin gabashin Azerbaijan har yanzu an kasa gano dalilinsa duk da sabon gwamnan ya taba aiki da jami'an tsaron kasar.

Wani rahoto ya bayyana yadda 'yan tawayen Syria suka taba garkuwa da sabon gwamnan, The Guardian ta wallafa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: ISWAP ta hallaka wasu jiga-jigan kwamandojin Boko Haram da mabiyansu 18

Bidiyon jami'in gwamnati yana tsinkawa sabon gwamna mari yayin rantsarwa a Iran
Bidiyon jami'in gwamnati yana tsinkawa sabon gwamna mari yayin rantsarwa a Iran. Hoto daga theguardian.com
Asali: UGC

Sabon gwamnan mai suna Birgediya Janar Abedin Khorram, ya hau kan mumbari a babban birnin yankin na Tabriz yayin da mutumin ya taso tare da falla masa mari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon da gidan talabijin na jihar suka fitar, ya nado yadda jama'a suka taru tare da bude baki jin irin zazzafan marin da ya fito daga lasifika.

An dauka dakiku kadan kafin jami'an tsaron farin kaya su garzaya tare da damke mutumin domin ceton sabon gwamnan

Jami'an tsaron sun damke mutumin tare da fitar da shi ta wata kofar gefe. Daga bisani an ga Khorram ya koma kan mumbari domin cigaba da jawabi ga hargitsatsun mutanen.

"Ban san shi ba gaskiya amma ina so ku sani cewa, duk da ba na son fadi kuma, lokacin da na ke Syria ana ba ni bulala goma kullum ko kuma a yi min dukan tsiya," yace

Kara karanta wannan

Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu

"Fiye da sau goma an rike bindiga a kai na. Na dauke shi duk daya ne da wadannan makiyan, amma na yafe masa," ya kara da cewa.

Duk da Khorram ya ce bai san mutumin ba, Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA ya bayyana mutumin da daya daga cikin sojojin Ashoura wanda Khorram ya taba shugabanta.

IRNA ta kwatanta farmakin da fansar wani abu da ke tsakaninsu duk da dai ba a kara bayani a kai ba.

The Guardian ta ruwaito cewa, daga bisani an gano cewa mutumin da ya tsinka wa gwamnan mari ya fusata ne bayan ma'aikacin jinya namiji ya yi wa matarsa allurar rigakafin korona ba mace ba.

Wani Mutum Ya Sharara Wa Shugaban Faransa Emmanuel Macron Mari

A wani labari na daban, wani mutum ya mari Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa a ranar Talata yayin da ya tafi ganawa da mutanen gari a yankin kudancin kasar kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna, France 24 ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Masu tsaron Macron sunyi gaggawa sun zakulo mutumin daga cikin dandazon mutane suka matsar da shi gefe. An kama wasu mutane biyu da hannu kan lamarin kamar yadda RMC radio ta ruwaito.

Reuters ta ruwaito cewa Farai Ministan Faransa Jean Castex ya ce lamarin karan tsaye ne ga demokradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng