Kotu ta hukunta wata mata dake duba wayar mijinta ba tare da izini ba

Kotu ta hukunta wata mata dake duba wayar mijinta ba tare da izini ba

  • Wata kotu ta yanke wa wata mata hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku bisa zargin keta sirrin mijinta
  • Matar dai tana ɗaukar wayar maigidanta domin binciken abinda yake aikatawa, shi kuma ya maka ta a Kotu
  • A cewarta ta yi hakane saboda zargin da take masa na cin amanarta da wayar

United Arab Emirate - Wata kotu a haɗaɗɗiyar dauƙar Larabawa (UAE) ta yankewa wata mata hukuncin zaman gidan kaso na tsawon wata uku saboda duba wayar mijinta ba tare da izini ba.

Aminiya Hausa ta rahoto cewa mijin ya kai ƙarar matar ne gaban kotu, domin a bi masa haƙƙinsa na duba wayarsa da take yi ba tare da neman izini ba.

Kotu a UAE
Kotu ta hukunta wata mata dake duba wayar mijinta ba tare da izini ba Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa kotun dake zamanta a yankin Ras a Al-Khaima ta kama matar dumu-dumu da laifin keta sirrin mijinta.

Kara karanta wannan

Hatta Mijina Yana Alfahari dani: Mahaifiyar Yara 2 Direban Tasi Ta Birge Jama’a a Bidiyo

Matar zata biya tarar kuɗi

Hakanan kuma kotun ta tuhumi matar da laifukan kwafar bayanan mijinta, hotuna da sauran wasu mu'amalansa ta hanyar amfani da wasu manhajoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan tabbatar da laifin matar, kotun ta yanke mata hukuncin biyan tarar kuɗi da suka kai kimanin AED 8,100.

Meyasa matar take duba wayar maigidanta?

A ɓangarenta, matar ta bayyana cewa tana duba wayar maigidanta ne saboda tana zarginsa da cin amanarta.

Ana ganin dai UAE na kan gaba wajen kafa dokoki masu tsauri, musamman waɗanda suka shafi mu'amalar aure da zamantakewa ta yau da kullum.

A wani labarin kuma Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

Wani magidanci a ƙasar Indiya ya nemi a raba aurensa da matarsa shekaru biyu da aure, saboda bata yin wanka kullum.

Kara karanta wannan

Kyari: NDLEA Bata da Hurumin Gurfanar dani, Ina Rokon Kotu Tayi Watsi da Kararta

Sai dai labarin baiwa matar ɗaɗi ba, inda ta garzaya wurin wata ƙungiyar kare mata, tana neman a ceto mata aurenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: