Sani Hamza
4971 articles published since 01 Nuw 2023
4971 articles published since 01 Nuw 2023
Yahuza Getso ya zargi hukumomin tsaro da sakaci bayan ya ba da rahoto cewa 'yan ta'adda za su kai hari Kebbi, lamarin da ya jawo har aka sace dalibai sama da 25.
Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da cewa adadin dalibai mata da 'yan bindiga suka sace a makarantar GCGSS Maga ya haura 25, sabanin rahotannin da ake yadawa.
Wasu daga cikin iyayen dalibai mata da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kebbi sun mamaye harabar makarantar. Wata mahaifiya ta ce ba za ta koma ba.
'Yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi a harin da suka kai cocin Kwara. 'Yan bindigar sun kashe fasto, kuma sun sace masu ibada masu yawa a yayin harin.
Gagarumar sauya sheƙa ta auku a Taraba yayin da shugaban PDP, kwamishinoni, ‘yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi suka bar PDP suka koma APC.
Umar Sani ya bayyana cewa Nyesom Wike ya bukaci PDP ta janye takarar shugaban kasa a 2027, ko kuma ta fuskanci rikici mai tsanani cikin jam’iyyar gabanin zaben.
Gwamna Agbu Kefas na Taraba ya dakatar da shirin shiga jam'iyyar APC sakamakon sace dalibai mata a jihar Kebbi. Ya yi kira ga hukumomin tsaro su gaggauta ceto yaran.
Gwamnatin Katsina ta umarci Malam Yahaya Masussuka ya kare kansa gaban malamai. Ana zargin karatuttukan malami sun sabawa koyarwar addinin Musulunci.
PDP, tsagin ministan Abuja, ta fatattaki gwamnonin Oyo, Bauchi da Zamfara daga jam'iyyar sannan ta tsige dukkanin shugabanninta a jihohi shida saboda wasu dalilai.
Sani Hamza
Samu kari