Abdullahi Abubakar
5748 articles published since 28 Afi 2023
5748 articles published since 28 Afi 2023
Jam'iyyar APC reshen jihar Benue ta gudanar da addu'o'i na musamman da malaman addini suka jagoranta domin samun nasarar Bola Tinubu da yaye matsalolin kasar.
Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Manjo-janar Muhammad Ilyasu Bashir ya taya Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II murnan dawowa kan kujerar sarautar jihar.
Wasu ƴan bindiga sun farmaki GRA inda suka sace lakcarori biyu ciki har da Farfesa da kuma ɗansa da ke Jami'ar Tarayya a garin Dutsinma da ke jihar Katsina.
Hukumomi a Jami'ar jihar Lagos sun yi martani bayan samun satifiket na digiri a hannun masu siyar da nama a jihar inda suka ce an dade da daukar mataki kan lamarin.
Kungiyar kwadago NLC ta fitar da sanarwa da safiyar yau Talata 4 ga watan Yuni kan ci gaba da yajin aiki inda ta ce sai an ji daga gare ta kan matakin da za ta dauka
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya magantu kan halin da ya shiga a gidan yari da ke Yola inda ya ce marigayi Lamidon Adamawa ya taimake shi a zamansa.
Yayin da ake tururuwa zuwa fadar Muhammadu Sanusi II, ƴaƴan Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun ziyarci fadar Sarkin tare da nuna goyon baya da addu'o'i gare shi.
Kungiyar Arewa Truth and Justice Initiative ta zargi Gwamna Abba Kabir da yin rufa-rufa wurin gazawarsa a mulki tare da mayar da hankali wurin rushe masarautu.
Mutane da dama a Kano sun fara shiga fargaba kan yawaitar ƴan daba a fadin jihar musamman saboda rigimar sarauta da ake yi inda suka bukaci karin jami'an tsaro.
Abdullahi Abubakar
Samu kari