Mummunan hatsarin mota ya afku a Jigawa

Mummunan hatsarin mota ya afku a Jigawa

- Wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Hadejia-Kano a jihar Jigawa yay i sanadiyar mutuwan mutane takwas

- Kimanin mutane hudu da abun ya cika da sune suka mutu a take bayan hatsarin ya faru

- Kakakin hukumar NSCDC na jihar ya bayyana cewa an kai gawawwakin wadand suka mutu asibiti

Mummunan hatsarin mota ya afku a Jigawa
Hoton wani htsari da ya afku

A kalla mutne takwas ne suka rasa rayukansu a wani mumunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Hadejia-Kano a jihar Kaduna.

An bayyana cewa hatsarin ya faru ne skamakon wasu motoci biyu da suka shige ma juna a kan babban titi, a karamr hukumar Kaugama dake jihar.

A cewar jaridar Independent, motocin sunyi karo ne lokacin da wani mota ya zo shan gabansu ba bisa ka’ida ba.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa bamu saki Sambo Dasuki ba

Da yake tabbatar da al’amarin, kakakin hukumar NSCDC na jihar, Adamu Abdullahi, yace jami’an NSCDC sun taimaka gurin ceto wadanda suka rayu yayinda aka kai wasu asibiti.

A cewar wani da abun ya faru a kan idanunsa hatsarin ya faru ne sakamakon wani mota da ya tawo da gudu yana kuma tukin ganganci da ya zo shan gaban motocin amma bisa rashin sani sai ya yi karo da wani mota.

Al’amarin mara dadin ji ya afku wasu yan kwanaki bayan mutane 15 sunji mummunan raunuka sakamakon wani babban mota da ya yi karo da pal wayan wuta a ranar Litinin 4 ga watan Oktoba a jihar Abia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng