Rikicin Oyegun da Tinubu: Atiku yace Tinubu na da gaskiya

Rikicin Oyegun da Tinubu: Atiku yace Tinubu na da gaskiya

- Tsohon mataimakin shugaban kasa mai suna Atiku Abubakar ya ga kira jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ta sake sabon zabe a jihar Ondo

- Atiku ya goyi bayan jigon jam'iyyar APC Sanata Ahmed Tinubu game da rikicin cikin gidan da ya afkawa jam’iyyar ta APC

– Tsohon mataimakin shugaban kasan yace abin da Cif Oyegun yayi bai dace ba

Rikicin Oyegun da Tinubu: Atiku yace Tinubu na da gaskiya
Raayin Bola Tinubu da Atiku Abubakar game da Oyegun ya zo daya

 

 

 

 

 

 

 

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar yayi kira da cewa APC ta soke zaben fitar da gwanin da tayi a Jihar Ondo, ta sake gudanar da wani sabon zabe. Tsohon mataimakin Shugaban Kasar ya goyi bayan Bola Tinubu, wanda yayi irin wannan kira, kwanaki biyu da suka wuce. Duk da cewa Atiku Abubakar din ya bayyana cewa matakin da Cif Oyegun ya dauka ba daidai bane, bai goyi bayan ya sauka daga matsayin nasa ba.

KU KARANTA: Bafarawa ya aika wasika ga Buhari

Jaridar Daily Trust ta Kasa, ta rahoto cewa Tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya kira Jam’iyyar su ta APC da ta gudanar da wani sabon zabe a Jihar Ondo. Rotimi Akeredolu ne ya lashe zaben, inda ya buge sauran ‘Yan takara da dama, daga ciki har da Olushegun Abraham-wanda ake tunanin Tinubu ya goya masa baya. Bayan an gudanar da zaben dai, kwamitin da suka yi aikin sun tabbatar da cewa an samu matsala a zaben, an karya sharudda wajen zaben, don haka suka nemi a shirya wani. Sai dai Shugaban Jam’iyyar APC bai yi hakan ba, ya tura sunan Dan takara Rotimi Akerodolu SAN zuwa Hukumar zabe ta Kasar.

Don haka ne dai Atiku Abubakar yake kira ga APC ta shirya sabon zabe kamar yadda aka nema. Yace bai dace ace Jam’iyyar tana karya dokokin ta, da kan ta ba. Yace tabbas za a samu matsala bayan yin hakan. Tsohon mataimakin Shugaban Kasar Atiku Abubakar, yace sam bai dace ace APC ta aika sunan dan takara Rotimi Akerodulu ba. Ya kira Jam’iyyar ta su da ta guji son kai da rashin adalci.

A makon nan dai, Bola Tinubu ya zargi Cif Oyegun da karya manufan da ta sa aka kafa Jam’iyyar saboda wasu kudi kankani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng