Mulkin Arewa a kasar Najeria tun 1960

Mulkin Arewa a kasar Najeria tun 1960

Dalilan da ya sanya yankin Arewacin Najeriya ta mulka kasar Najeriya fiye da sauran yankuna tun bayan da aka samu yancin kai, a watan Oktoba ta shekara 1960.

1. Bambanci

Ta fannin bambanci, yankin Arewa na da girma fiye da sauran yankunan Najeriya wannan yana daga cikin abubuwan da suka ba Arewacin Najeriya daman mulkan Najeriya fiye da sauran yankuna.

2. Addinin Musulunci

Addinin Musulunci da aka kafa tun kafin zuwan turawa, da kuma yaren Hausa, wanda ya zama harshen tarayyar al’umma.

Shugaban Fulani, Sultan na Sakkwato da kuma Shehun Borno, wannan khalifofin addinin Musulunci sunyi kokari gurin hada addinin Musulunci da shugabanci wannan ya basu damar yi wa sauran sassan kasar nisa ta fannin shugabanci, domin kamar yadda muka sani a siyasar Najeriya, addini na taka muhimiyar rawa, domin kowa zai so ace addininsu daya da mai mulkar kasar. Kuma kamar yadda muka sani musulmai sunfi yawa a kasar ta Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya halarci taro a majalisar dinkin duniya

3. Kabilanci

Kabila wani dama ne ga Arewa ta fannin cin ribar siyasa (shugabanci), kabilu dake a Arewa sun kai kimanin kaso biyu cikin uku na kasar, wanda suka hada da yaren Hausa, Fulani, wanda yawancinsu Musulmai ne da kuma sauran kabilu kamar su Nupe, Kanuri da sauransu. Kuma, kamar yadda siyasar Najeriya take ko wacce kabila tana so ace dan kabilarta ne ya yi nasarar lashe shugabanci.

Mulkin Arewa a kasar Najeria tun 1960
Muhammadu Buhari (hotunansa a lokacin gwamnatin soja da kuma a lokacin kamfen a 2015)

Wannan ne yasa yan arewa suke fitowa da kwansu da kwarkwatarsu don goyon bayan shugabannin Arewa har sai sunyi nasara.

4. Dangantaka

Kusanci dake tsakanin jihohin Arewa da kuma yankin Najeriya maso tsakiya (Central Nigeria Area) yana daga cikin dalilan da yasa Arewa ke nasarar mulkar Najeriya fiye da sauran yankuna.

5. Noma

A Arewacin Najeriya, akwai gonakai masu girma wanda ke dacewa da noma, don haka yankin ya kasance matattarar abincin kasar. Kayayyakin abincin yankin yana rayar da sauran yankuna wannan na daga cikin dalilan da ya basu damar tafiyar da kasar a karkashin su.

KU KARANTA KUMA: Malamin makarantar sakandire ya lalata dalibarsa

6. Yawan mutane

Filayen yankin Arewa ya fi na sauran yankunan girma wannan ne ya bata damar daukar mutane da yawa, hakan ya dada taimakawa gurin basu nasarar mulkar kasar, domin anyi itifakar cewa yan Arewa sunfi kowa yawan mutane a kasar Najeriya a lokacin da akayi kididdigan munate (census).

7. Sanin makamar mulki

Tun kan zuwan turawan mallaka kasar Najeriya, yankin Arewa tayi mu'amala da larabawa, harma ta koyi yanayin mulkinsu, wannan ne ya bata damar sanin makamar mulki fiye da sauran yankunan kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel