Kiristoci su daina saki inji Fasto Crist

Kiristoci su daina saki inji Fasto Crist

Babban Faston Najeriya kuma wanda yake da 'dinbin mabiya, kuma jami'in Loveworld sannan wanda akafi sani a Crist Embassy, yayi ma kafaffen yada labarai bayani.

Kiristoci su daina saki inji Fasto Crist

Haka kuma, ya zargi kafaffen yada labarai akan abin da suke fadi a kansa, yace yawancin abubuwan da ake fadi akansa karya ne.

Ya kara dacewa, " Na fahimci wasu gidajen kafofin yada labarai, musamman a nan Najeriya, sannan kuma a kasar Afirika ta kudu suma suna rubuta wani abun banza a kaina wanda bai kamata ba, abune na wayau.

Ni banyi wa'dannan abubuwan da kuke fadi ba, kuma ban aikata duk wa'dannan abubuwar da kuke fadi nayi ba, haka kuma niba mai wa'azi bane, ni mutumin Allah ne.

Akan makagar Reberal Anita kuwa, ayi mata addu'a, idan mace ta auri mutumin Allah, to wannan bashi ke nuna cewar kin zama babba ba kenan, zaki iyayin kuskure".

" Sannan ya kara dacewa kiristoci su daina saki, kada suyi haka, amman wannan bashi ke nuna cewar kiristoci kada su dauki wannan matakin ba, ah'ah, zasu iya, amman hakan bai kamata ba, kuma kada mukai junan mu kotu, saidai idan hakan ya faru, to bamu zamuje ba, wani zai kaimu can wajen.                                              Wannan shine matsalar.

Hmmm, yayi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng