Uba ya mutu a gurin bikin yar sa

Uba ya mutu a gurin bikin yar sa

-Tim Buchanan yaje taya yarinyar sa bikin aurenta a Costa Rica

-Bayan rawa tsakanin  ya da uba, ya kamu da ciwon zuciya inda ya mutu jim kadan bayan nan

Uba ya mutu a gurin bikin yar sa

Wani dan sanda a Kudancin Crolina, na kasar Amurka Tim Buchanan mai shekaru 54 a duniya, wanda ya halarci auren yarsa a Costa Rica a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba. Amma akayi rashin sa’a, jim kadan bayan sun gama rawa tare da yar tasa, ya kamu da ciwon zuciya wanda yabar iyalansa cikin mamaki da jimami.

KU KARANTA KUMA: Mutuwa ta raba ma’aurata da sukayi shekaru 77 tare

Matar sa, Jeni Buchana ta sanar da mutuwar tasa cikin wani rubutu da tayi a shafinta na Facebook kamar haka. Tace: “Bazaka taba sanin lokacin da zai zamo na karshe a rayuwar ka ba! Tim ya jigo cikin rayuwata a lokacin da na karaya ainun ya kuma tallafa mu har na zama mutun mai karfi.

 “Cikin shekarun da mukayi tare mun raini yara hudu, kula da kanne na maza a lokacin da sukafi bukatar mu harma da alfarman kyawawan jikoki.”

Uba ya mutu a gurin bikin yar sa

 “Shine ruhi mafi kyau ta na taba sani kuma bazan taba kasancewa yadda nake a da ba tare da shi ba. Na san ya soni da yan uwana. Ina mai godiya kan wannan hoto namu da abokanmu Kelly Rae Stewart da mijinta suka dauke mu a lokacin auren yar mu a jiya. Ba tare da na san cewa dan sa’o’I kadan ya rage mana mu rasa shi ba.”

KU KARANTA KUMA: ku dubi matashiyar da ta haifi yara 9 (hotuna)

Sheriff Bruce Bryant tayi Magana ga mujallar PEOPLE cewa: “Zuciyoyinmu dukka na cikin bakin ciki game da wannan babban rashi na jami’in doka da munakyi. Tim ya sadaukar da kusan shekaru goma sha tara (19) a wannan aiki a matsayin mataimakin shugaban masu bincike mai kwazo. Babu shakka zamuyi rashin baiwar sa. Addu’oin yana ga iyalansa a wannan hali na kunci da wahala da suke ciki.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng