Najeriya na jiran Ndigbos - Okorocha

Najeriya na jiran Ndigbos - Okorocha

- Gwamna Okorocha na bayyana fatarsa wajen ci gaban Ndigbo

- Ya kira hakan aikin dake ci gaba

- Jim Nwobodo yace yana mai kaunar hazakar Okorocha wajen ganin nasarar Ndigbo

Rochas Okorocha ya bayyana fatarsa na habakar Ndigbos a Najeriya yace kuma Najeriya na jiransu

Najeriya na jiran Ndigbos - Okorocha

Vanguard ta ruwaito gwamnan jihar Imo na fadin ra'ayinsa yayin da yake karbar matan gwamnonin jihohin kudu maso gabas lokacin da suka iso jihar domin taron watan Agusta na wannan shekarar. Rochas Okorocha ya ba matan shawara da su kara hakuri, yana cewa aiki ne mai ci gaba. ya kara da cewa:

"Kabilar Igbo wata halitta ce ta dabam ta Ubangiji. Najeriya na jiran Ndigbo, Afrika na jiran Ndigbo. Ina ma Ndigbo ganin fa'ida. A duk tarurrukan da muke yi wannan yafi su duka. Ba wani abinda namiji zai iya yi ba tare da mace tagari a bayansa ba.  Ina karfafa gwuiwowin mata a cikin gwamnati na da shirye-shirye na da manufofina"

Jim Nwobodo wanda ya shugabanci bukin kuma tsohon gwamnan Anambra yace yana nadamar rashin ganin ci gaban Igbos duk da ayyukan da yayi nagari yayin mulkinsa. Yace abinda ya tilasta masa goyon bayan Okorocha ke nan wanda yayi amanna zai kai ga biyan bukata.

KU KARANTA: Najeriya na jiran Ndigbos-Okorocha

"Ban halarci wani ba baya ga wannan da yake na musamman. Nazo nan domin Okorocha mai hazaka ne da hangen nesa a madadin kabilar Igbo. Kowannenmu da ya shugabanci kasar nan a kowane hali mun galabaita domin kasancewarmu Igbos. Ya kamata mu hada kanmu. A kasar Igbo, muna kaunar mata kwarai yadda duk abinda akayi ba mata to bashi da nasara. Ina zaton Okorocha ya fahimci abin sosai. Kayi tunanin zuwa neman kuri'a, sai mata suce zasu zabe ka. Ka tabbatar kana da kuri'unsu."

Mrs. Josephine Aninih, a maganarta ta godiya, ta bukaci gwamnan ya kokarta wajen hada kan mazan Igbo domin ci gaban yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel