Fulani makiyaya sun kai hari ga Fayose kan dokar kiwon dabbobi
- Fulani makiyaya sun maida martani ga dokar kiwon dabbobi da aka kafa a kwanan nan, wanda ya haramta wa makiyaya daukar makamai da yawo da dabbobi a jihar Ekiti
- Makiyayan sun ki yin biyayya ga dokar, sunyi ikirarin cewa babu wanda za’a caja da laifin ta’addanci don ya dauke adduna, bari da maka, da kuma wukake a lokacin kiwo
Fulani Makiyaya mazaunar jihar Ekiti da suka fito daga garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, karkashin laimar kungiyar Jamu Nate Fulbe na kasar Najeriya sun ki amincewa da sabon dokar kiwon dabbobi da gwamna Ayodele Fayose ya kafa.
KU KARANTA KUMA: Ina alfahari da harshen Hausa- wanda ya kafa Facebook, Zuckerberg (Hotuna)
Mai bada shawara ga makiyayan a harkan shari’a, Mr. Umar Imam, ya jadadda haramcin daukar kananan makamai kamar su adduna, wukake, bari da maka da kuma kibiyoyi, yayi Magana game da rigakafin ta’addanci na shekara 2011.
Ku tuna cewa dokar me taken “haramta kiwon dabbobi a jihar Ekiti, shekara ta 2016” yayi tanadi cewa dole ayyukan kiwon dabbobi ya fara daga karfe bakwai (7) na safe zuwa karfe shidda (6) na yamma a kullun, yayinda daukar makamai zai zama a matsayin ta’addanci.
Mallam Umar Imam, yayi Magana a kan dokar a ranar Laraba: “Dokar tarayya a kan ta’addanci a bayyane yake kuma babu wanda za’a caja da laifin ta’addanci saboda ya dauki kananan makamai kamar su adduna, bari da maka, da kuma wukake a lokacin kiwo kamar yadda yake a sabon dokar jihar Ekiti.
“Na bayyana a bainar jama’a da naji dokar a majalisar jihar Ekiti cewa wadanan Fulani Makiyayan suna amfani da wadanan kananan makamai ne domin wasu dalilai cewa wannan yana saukaka masu kiwo.
“Na kuma fada masu cewa wannan tafiya da sukeyi da daddare yayinda zasu canja waje saboda su tabbatar da cewa basu halakar da mutane da rana bane. Na so naji cewa gwamnatin jihar ya dauki nauyin wannan a sabon dokar sa maim akon ya hana gaba daya.
“Mun yarda da dokar gwamnan na kiwo daga karfe 7 na safe zuwa 6 na yamma amma a bari mu dauki kananan makaman mu da kuma canja guri da daddare.”
Asali: Legit.ng