Dan wasa Ibrahimovic na shirin kafa tarihi a Man Utd

Dan wasa Ibrahimovic na shirin kafa tarihi a Man Utd

– Zlatan Ibrahimovic ka iya rubuta sunan sa cikin tarihin Kungiyar Man Utd.

– Dan wasan na bukantar kwallo daya rak, ya karya tarihin shekaru 91 a Kungiyar.

– Kwararraen dan wasan gaban ya ci kwallaye har kusan uku da suka ba Kungiyar sa nasara, kawo zuwan sa Kulob din.

Dan wasa Ibrahimovic na shirin kafa tarihi a Man Utd

Kwararren lamba taran nan na Man Utd na bukatar kwallaya daya kacal domin ya ajiye tarihin da ya fi tsawon shekaru 90 da Kungiyar.

Idan har Sabon Dan Wasan Kungiyar Man Utd dinnan, Zlatan Ibrahimovic ya jefa kwalla guda a wasan su na gaba, to ya karya wani tarihi na kusan shekaru 100 a Kungiyar. Man Utd za dai ta kara ne da Kungiyar Hull City a ranar Asabar mai zuwa, 27 ga Watan Agusta.

Dan wasan ya komo Kungiyar ta Man Utd ne daga Paris Saint Germain wannan shekarar, tun zuwan sa kuma, dan wasan ya zuba kwallaye uku cikin wasanni biyun da ya buga. Idan kuwa har dan wasan ya samu ya leka zare a wasan sa na uku (wanda za a buga da Hull City na ranar Asabar), zai ajiye tarihin da wani tsohon dan wasan Kungiyar ya taba bari.

Wani Dan wasan mai suna Jimmy Manson ya bar wannan tarihi ne a shekarar 1924/1925. Dan wasa Mason dai, shi kadai ne wanda ya taba zuba kwallaye a wasanni ukun farkon da ya buga bayan ya komo Kungiyar.

KU KARANTA: KOCIN INGILA ZAI AJIYE DAN WASA RASHFORD

Dan wasa Zlatan mai shekaru 34 a duniya dai ba ya nuna alamun tsufa ko gajiya a tare da shi ko kadan, har kuwa ma ya jefa kwallaye da dama daga zuwan sa; Wasan Bournemouth Southampton da Leicester. Kwallon da dan wasan ya ci tsakanin su da Southampton, ita ce kwallo ta 400 da dan wasan ya ci a rayuwar sa. Wannan mako ne kuma za su kara da Hull City, Hull City dai tana tare da Man Utd a samun teburin Gasar Premier league.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: