Dalilin da yasa mata suke sanya mayafi a ranar Aurensu
-Mata a Najeriya suna sanya mayafi tun lokacin da aka gabatar da auren turawa a lokacin mulkin mallaka
-Dalilin da yasa mata ke sanya mayafi ya sha bambam daga al’ada zuwa al’ada
-Farin shamaki ko mayafi wani alama ne dake nuni ga tsarki
Da yawan matsalolin gargajiya yana zuwa ne lokacin bikin aure. Wani al’amari ne “ga yanda ake yi”. Wanda yafi yawa a ko ina tun lokaci mai tsawo a al’adun gargajiya shine amarya ta rufe kanta da mayafi.
Wannan ya zama wani koyi na al’adu da dama da kuma addinai tun lokacin kakkani kuma har yau ana aikata shi sosai. Ya hade a cikin sananun addinai da al’adun yawancin al’umma amma har yanzu babu wanda ya tambayi dalilin da ya sa amarya ke sanya mayafi a ranar aurenta.
Duk da haka, hukumar Legit.ng tazo domin ta wayar maku da kai.
Asalin Sanya mayafi amare ya samo asali ne daga zamanin Romawa. Littafin tarihi ya nuna labarum amfani da mayafi a matsayin hanyar raba matan aure daga marasa aure. Tun daga wannan aya har yanzu an koyi amfani da mayafi da ma’anoni daban-daban amma dai ana ci gaba da amfani da shi.
KU KARANTA KUMA: Yawancin bankunan Liberia mallakin yan Najeriya ne- Boakai
Ana kuma amfani da shi domin”kore mugunta.” Ana rufe amaren Romawa da dogon mayafi ja a kokarin bayyanasu kamar suna kan wuta domin a kori mugayen aljanu. Hakika, an daina wannan a yanzu.
Addinin Kirista tana amfani da mayafi a matsayin wani alama na tsarki, wannan ne yasa suke yawan amfani da farin mayafi. Suna sanya farin mayafi mai shara-shara tare da kayan aurensu, wannan yana nuni ga cewa “matancin” amaryan na nan daidai.
Asali: Legit.ng