Buhari yayi magana akan kisan Jihar Zamfara

Buhari yayi magana akan kisan Jihar Zamfara

–Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kisan Wadanda sukayi maganar batanci ga Annabi Muhammadu (S.A.W) .

–Anyi wa dalibi dukan kawo wuka kuma an banka ma wasu 8 wuta har lahira.

Buhari yayi magana akan kisan Jihar Zamfara

A yau talata,23 ga watan augusta, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kisan mutane 8 a Jihar Zamfara sanadiyar wata tarzoman addini da ya faru a makarantan Abdu Gusau a Jihar Zamfara.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne ta shafin sada zumuntar sa ta twita.

" Na samu labarin kisan da ya faru a jihar zamfara . wannan shirme ne kuma bazamu yarda da shi ba. Ina daukan alwashin cewa za'a dau mataki. Ina nuna juyayi na ga iyalan Wadanda suka rasa rayukansu.

KU KARANTA : Najeriya ta karaya sosai a yanzu, Obasanjo yayi kashaidi

Dalibin yayi maganan batanci ne ga Annabi Muhammadu, sai sai aka masa dukan rabani da yaro. Wani mutum mai suna Tajudeen sai ya ceto shi ya kaishi asibiti. Matasan sai suka afka gidan Tajudeen suka banka masa wuta, mutane 8 ne suka kone a gobarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel