Boko Haram sun bar Sambisa sun koma dajin Burra a jihar Bauchi

Boko Haram sun bar Sambisa sun koma dajin Burra a jihar Bauchi

-Kungiyar Islama, na Boko Haram sun kafa wani sabon tushe a jihar Bauchi

-Sanata Isa Hamma Misau wanda ke wakiltan jihar Bauchi na tsakiya a majalisar dattawa ne ya bayyana haka

-Dajin Sambisa ta kasance matattarar yan ta’adda

Sanatan dake wakiltan jihar Bauchi na tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Isa Hamma Misau ya bayyana cewa kungiyar Yan ta’addan Boko Haram sun kafa sabon tushe a garinsa jihar Bauchi.

Boko Haram sun bar Sambisa sun koma dajin Burra a jihar Bauchi
Senata Isa Hamma Misau

Sanata Misau, wanda ya kasance babban jami’in dan sanda (Mai ritaya) ya bayyana wa jaridar Daily Trust a kan waya cewa kungiyar yan ta’adda sun kafa tushe a dajin Burra a yankin masarautar Ningi wanda ke karkashin yankin da yake wakilta a majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai cika dukkan alkawuran zaben sa

A cewar Sanatan, yan ta’addan sun bayyana wa wadanda abun ya shafa cewa sun bar gurin da aka fi sanin su wato dajin Sambisa, wanda ya kasance ainahin tushensu kafin sojojin Najeriya su kai masu hari.

Sanatan ya sha alwashin dauko lamarin a taron yan majalisat dattawa na sabon wata duk da yayi alkawarin rubata wasika ga dukkan hukumomin tsaro a kasar domin su kawo dauki a cikin lamarin.

A halin yanzu, babban hekwatan masu tsaro a jiya 9 ga watan Augusta sun tabbatar da cewa kungiyar yan ta’addan Boko Haram wadanda suka bar jihar Borno sun kafa wani sabon tushe.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng