Rio Olympics: Tawagar Najeriya ta je ba da Iheanacho ba (Karanta dalili)

Rio Olympics: Tawagar Najeriya ta je ba da Iheanacho ba (Karanta dalili)

Matashin dan wasan gaban nan na kungiyar Super Eagles ta kasar Najeriya Kelechi Iheanacho ba zai bugama kasar tasa gasar Olympics din da za'ayi garin Rio na kasar Brazil ba kwanan-nan sakamakon sanya shi da kungiyar tasa ta Manchester City tayi a cikin tawagar ta da zasu je buga wasannin share fagen kakar wasa mai zuwa.

Shi dai mai horarwar kulob din na Man City Pep Guardiola ya fitar da jerin sunayen yan kwallon da zai tafi dasu wasannin share fagen kuma abin mamaki hadda sunan Iheanacho din. Dama dai tuni wasu yan kasar suka nuna shakkun su game da yiwuwar dan wasan mai shekaru 19 ya bugawa kasar tasa gasar a cikin wata mai kamawa na Agusta.

Rio Olympics: Tawagar Najeriya ta je ba da Iheanacho ba (Karanta dalili)
kelechi Iheanacho, Odion Ighalo and Alex Iwobi in training

Yanzu dai Iheanacho zai hadu ne shahararrun yanwasan kungiyar ta Man city irin su Sergio Aguero, David Silva, Joe Hart da Vincent kompany a cikin wasannin da za suyi da wasu kungiyoyin kamar su Bayern Munich, Borussia Dortmund dama Manchester United.

Amma kuma dai kulob din na Man city sun fa wasu yan wasan su kamar su Otamendi, Raheem Sterling da Nolito karin hutu don saboda gasar nan ta cin kofin kasashen turai da suka buga a kwanakin baya. A wani labarin kuma shi dai Iheanacho din ya zura kwallaye 14 ne a kakar wasannin da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel