Kashi 53% sun samu nasara a Jarabawar WAEC
– An samu karuwar wadanda suka ci Jarabawar WAEC (May/June) a Najeriya wannan karo.
– Wani Jami’in Hukumar ta WAEC yace za ayi bincike dangane da sakamakon jarabawar wasu da aka rike.
Kimanin kaso 53 (bisa 100) sun samu nasara a Jarabawar WAEC (ta May/June) da aka rubuta na shaidar kammala karatun sakandare na Afrika ta yamma (WASSCE) a wannan shekara ta 2016. An fitar da sakamaon jarabawar ne a ranar Juma’a nan. An dai rike sakamakon jarabawar mutane 137, 295. Daliban da suka samu makin da ake bukata kuwa sun kai 878,000. Kason wanda suka samu makin kiredit din da ake bukata (wanda ya hada da darasin Turanci da lissafi) ya kai 52.97, hakan ba karamin cigaba aka samu ba idan aka kamanta da shekarun baya. A 2014, kashi 31.28% kacal suka samu nasara, a shekarar 2015 kuma aka samu kaso 38.63% masu takardu biyar.
KU KARANTA: HUKUMAR NDLEA TAYI MUGUN KAMU
Shugaban Hukumar na Najeriya, Olu Adenipekun ya bayyana cewa ana binciken sakamakon jarabawar da aka rike, kuma kwamitin da ke wannan aiki za ta dauki mataki lokacin da ya dace, jaridar Vanguard ta rahoto. Bayanai sun nuna cewa cikin yan makaranta 1,552,758 da suka zauna jarabawar a wannan shekara. Mutane 1,370,049 suka samu cin kwas akalla uku, haka kuma guda 1,438,679 suka samu nasara a kwas akalla biyu. Ciki dai har wa yau, an samu guda 1,014,573 da suka yi nasarar samun kiredit a darussa har shida, kana guda 1,167,484 sun lashe kwasa-kwasai har biyar. Wadanda suka samu cin takardu hudu kuwa sun kai har 1,282,204.
A wannan yanayi dai, Fabian Benjamin na Hukumar JAMB ya bayyana ka’idojin da za a bi wajen daukan dalibai a makarantun gaba da Sakandare wannan shekara ta 2016.
Asali: Legit.ng