Abin da ya sa ba za mu iya hukunta Jibrin ba-APC
– Shugabannin Jam’iyyar APC ta ce ba aikin ta ba ne yanke hukunci dangane da batun zargen badakalar kasafin kudi a Majalisar Kasar.
– Jam’iyyar ta APC mai mulki, ta musanta batun cewa tana shirin hukunta Hon. Jibrin saboda zargin Shugaba Dogara.
– Har yanzu dai ba a samu an shawo kan wannan matsala ba.
Dalilin takkadamar da ke faruwa tsakanin ‘ya ‘yan Majalisar Tarayya, musamman tsakanin tsohon Shugaban kwamitin kasafi Hon. Mumini Jibrin da kuma Shugaba Dogara Yakubu, Jam’iyyar APC mai mulki ta gana da dan majalisa Hon. AbdulMumini Jibrin a jiya. Jibrin din ya gana da APC ne a saktariyar ta dake Abuja. Jama’iyyar dai ta aika ma Hon. Jibrin takarda ne, bayan da aka neme sa a waya, aka kasa. Hon. Jibrin kuwa yace, ya kashe wayoyin sa ne gudun ka da Dogara Yakubu ya sa a sace sa. Dan Majalisar mai wakiltar Kiru da Bebeji na Kano, ya gana da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar (Yankin Arewa), Lawal Shuaibu da kuma Sakataren APC, Mai Mala Bunida kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na bangaren Arewa maso-yamma, Inuwa AbdulKadir.
KU KARANTA: APC TA SAMMACI HON. ABDULMUMIN JIBRIN
Lawal Shuaibu ya bayyana cewa, haka APC ta gana da Shugaban Majalisar, Dogara Yakubu, kuma jam’iyyar ba ta da hurumin zartar da hukunci gare su. Har way au Shugaban Jam’iyyar ya bayyana cewa, APC ba ta da niyyar hukunta Jibrin dangane da zargen da yake ma Shugaban Majalisar Dogara, da ma wasu ‘yan Majalisun a kafafe da dama. Lawal ya bayyana cewa, za a cigaba da tattauna da ‘yan Majalisun biyu, Dogara da Jibrin, har sai an sama sulhu, amma dai kawo yaznu Jam’iyyar APC tace dai ba a samu damar sasanta su ba.
Shi dai Hon. Jibrin yace ba wani kwamitin horo da ladabtarwa da ta kira sa, ya gana ne da Shugabannin Jam’iyya kurum game da abin da ke faruwa.
Asali: Legit.ng