Cristiano Ronaldo ya sayi sabuwar motar Bugatti

Cristiano Ronaldo ya sayi sabuwar motar Bugatti

LABARIN WASANNI

CRISTIANO RONALDO YA SAYI MOTAR BUGATTI

Cristiano Ronaldo ya sayi sabuwar motar Bugatti

Kyaftin din Kwallon Kafar Kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya saye wata mota mai tsadar tsiya, da ake kira Bugatti. Ana tunani dai motar za ta kai fam miliyan 2.5 na Kudin Euro (Watau fiye da Naira Miliyan 700 kenan na Najeriya). Tauraron dan wasan na duniya, Cristiano Ronaldo ya jagoranci Kasar sa ta Portugal ta lashe gasar EURO da aka kammala kwannan nan a Kasar Faransa. Shi kan sa dan wasan na Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya misalta motar da ‘dabba’ yayin da aka kawo masa ita. Tsohon dan wasan na Manchester United ya bayyana haka a shafin sa na Kafafen zamani cewa, ‘Dabbar fa ta iso!’

Motar dai har yanzu ba ta da yawo a duniya, bari ma, sai dai mutum ya bada oda sai a kero masa ita. Shiyasa ake tunani wanda dan wasa Cristiano Ronaldo ya saya sai ta fi wanda za ta shigo kasuwa tsada. Da masana harkar motoci suka yi lissafi motar za ta kai akalla fam miliyan biyu da rabi (na Kudin Euros). Ga dai farashin kayayyakin (jikin) motar ta Bugatti:

– Asalin kudin mota (ba tare da haraji ba): Euro Miliyan 1, 600, 200

– Haraji (kasha 35.75%): Euro 700, 000.

– Kudin Rajista (A Birnin Madrid): Euro 230, 000

– Kudin Tayoyi: Euro 27, 000.

– Kudin Tayoyi na Sifiyo: Euro 60, 000.

– Kudin canja tayoyin: Euro 108, 000

– Kudin sabis: Euro 27,000

– Kudin juye (Na mai): Euro 18, 000

Ko tayoyin motar kadai, sai a Kasar Faransa ake cire su. Kuma ana bukatar tayoyin seto uku. Kuma Harajin da ake biya na motar ya kan fi na sauran motoci, saboda hayakin da ta ke fitarwa.

Idan dai an dawo gasar wasa, za a kara tsakanin dan wasa Cristiano Ronaldo na Real Madrid da Lionel Messi na Barcelona a ranar 3 ga watan Disamba na 2015 a filin wasa na Camp Nou da ke Birnin Barcelona, kana a kara haduwa a ranar 23 ga Watan Afrilun 2017 a Santiago Bernabeau da ke Birnin Madrid na Kasar Spain. Yawanci wanda yaci wasan El Clasico dai shi ke samun nasarar lashe gasar Kasar ta La-liga.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng