Mun sa kafar wando daya da Dino Melaye- Tinubu

Mun sa kafar wando daya da Dino Melaye- Tinubu

–Sanata Dino Melaye ya tono fadan ,babban jigon jam’iyyar APC,Bola Ahmed Tinubu, yayinda yayi barazanar dukan matanshi,Senata Remi Tinubu.

–Dino Melaye yayi barazanar zai doki Oluremi Tinubu kuma yayi mata ciki.

Mun sa kafar wando daya da Dino Melaye- Tinubu
remi tinubu

An zana filin daga tsakanin babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da hatsabibin sanata mai wakiltar mazabar kogi ta yamma,Dino Melaye. Yayinda dino melaye yayi wani halin rashin hankali na zagin sanata ‘yar uwarshi. Melaye ya dade da kasancewa wani hatsabibin dan siyasa. Lokacin da dan majalisar wakilai, yayi dambe da wasu abokan aikinshi.

Shi kuma Tinubu yace bayyana cewa akan abinda ya faru a majalisa na maganan batanci da dino ya ma matarsa, daga yanzu sun sa kafar wando daya da Dino Melaye. Ya fadi hakan ne ta mai Magana da yawunsa , Sunday Dare. Ya kuma shellanta cewa wannan shine karshen dino melaye a siyasar Najeriya.

Mun sa kafar wando daya da Dino Melaye- Tinubu
Senator Dino Melaye

Sanatocin guda 2 sun sami sabani ne ranar talata,12 ga watan yuli,yayinda sanatoci ke tattaunawa akan laifin aikin jabun dokokin majalisan dattawa da Shugaban majalisar,Bukola Saraki,da mataimakinsa,Ike Ekweremadu,da kuma wasu guda iyu suka yi.

KU KARANATA : Amurka za ta gabatar da shaida kan ‘yan majalisa

An ruwaito cewan Dino Melaye yayi barazanar dukan Sanata Remi Tinubu. Kuma yayi wasu maganganun batanci akan matan ,har da cewan zai mata ciki. Amma Dino Melaye ya musanta cewa ya fadi hakan. Dino Melaye ya fusata ne yayinda Oluremi Tinubu ta ki shawarar da yayi na cewan su fara shirin tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bola Tinubu yayi gargadin cewa sai ya yayi biji biji da melaye idan yayi kokarin taba matarsa.

Dare ya fadi hakan ne ta shafin sadarwa shi ta twita: “ Dino melaye ya tono idon tururuwa. Daga ya shiga uku. Abin kunya ne ga majalisan dattawan najeriya. Kuma idan yayi tunanin ba abinda zai faru idan ya doke wani sanata,to lallai wawa ne. abubuwa zasu faru.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng