Najeria na iya shiga rikicin siyasa-Pada Ebenezer
-Limamin cocin Assemblies of God a Najeria ya hango cewa Najeria zata iya shiga rikicin siyasa
-Amma limamin addinin yana mai cewa kasar ba zata mutu ba domin Allah zai warkar da ita
Pada Kingsley Ebenezer na cocin Assemblies of God na Najeriya ya aiko ma Legit.ng da abin da dubar shi ta nuna masa game da Najeria. Ya rubuto cewa "tsarin siyasar kasar na cikin hadari domin wani Sabon tsarin na iya mamaye shi.
Allah zai warkar da Najeria. duk da yake kasar zata fuskanci matsaloli masu yawa amma ba zata mutu ba domin Allah zai warkar da ita. "Gaya ma mutane na, su rika yin maganar Najeria da kalamai na gari domin makomarta na hannu su".
KU KARANTA : Kungiyar CAN sun kai hari ga Shugaba Buhari
Cocin Assemblies of God a Nageria nada mabiya wanda yawansu ya kai miliyan 3.6, wadanda ke ibada acikin majami'u 16,300 da ke cikin kasar. Cibiyar cocin na garin Enuga a jihar Enugu, tana da limamai 15,650 wadanda 50 daga cikinsu na kasashen ketare guda 9 a duniya.
Asali: Legit.ng