Har a cikin kewaye Cristiano Ronaldo na yin atisaye- Jose Fontes

Har a cikin kewaye Cristiano Ronaldo na yin atisaye- Jose Fontes

– Ronaldo tun yana yaro ya saba yin atisaye fiye da na sauran ‘Yan uwan sa.

 – Jose Fonte ya bayyana Ronaldo a matsayin mutum mai matukar hazaka.

 – Fonte yace dan wasan na Real Madrid bai bari sunan da yayi a duniya ya rufe masa idanu ba.

Har a cikin kewaye Cristiano Ronaldo na yin atisaye- Jose Fontes

 

 

 

 

 

Kyaftin din Kulob din Southampton na Ingila, Jose Fonte yace tun Cristiano Ronaldo yana dan yaron sa yake mai matukar kokari a filin wasa. Jose Fonte wanda shima yake buga ma Kasar Portugal tare da Ronaldo ya taba zama kulob daya tare da dan wasan a Kungiyar Sporting can baya, sai ga shi yanzu sun kara haduwa wajen buga ma gida. Kyaftin din Southampton ya bayyana waye asalin Cristiano Ronaldo da yadda aka yi har ya zama gwarzon duniya. Fonte yace tun a wajen horo, Cristiano Ronaldo zai ce ‘Yau sai na fi ku bada himma!’, kuma hakan za ayi, har a dakin wanka Cristiano Ronaldo baya barin atisaye. Haka Cristiano Ronaldo yake, baya so ya ga wani ya wuce sa a komi, shi ya say au ya zama dan kwallon duniya. Jaridar Daily Telegraph ta buga wannan labari

Jose Fonte yace: “Lionel (Messi) na burge ni, amma dai Cristiano Ronaldo dabam ne. Tun yana yaro, Cristiano zai tsaya a fili bayan kowa ya tafi gida domin ya cigaba da atisaye. Cristiano Ronaldo ba dai himma ba, ba za a hada sa da kowa ba.” Inji Fonte. Dan wasan ya kara da kuda dan Kasar sa yana cewa: “Cristiano Ronaldo bai bari sunan da yayi ya rufe masa ido ba domin kuwa duk inda kaje a fadin duniyar nan, babu inda ba a san sa ba, jama’a kowa na son sa.” Jose Fonte dai yace yana mai matukar alfahari ace Kasar sa daya da dan wasa Cristiano Ronaldo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel