Zahara Buhari ta dauki hoto tare da Baban Ta

Zahara Buhari ta dauki hoto tare da Baban Ta

Zahara Buhari ta dauki hoto tare da Baban Ta.

Zahara Buhari ta dauki hoto tare da Baban Ta

 A ranar Lahadin da ta gabata ne na 19 ga watan Yuni nan, fadin mutanen duniya aka yi bikin murnar Iyaye Maza.

Wasu sun yi amfani da ranar wajen nuna godiya ga mahaifan su kan dawainiyar da suka yi masu ko ma ake kan yi da su cikin shekaru. Wasu kuma da mahaifan nasu suka riga suka rasu, sun nuna ta’aziyyar su a gare su.

Wajen taya mahaifin ta murna, ba a bar ‘yar lelen Shugaban kasar Najeriya a baya ba, Zahara Buhari, ita ma ta nuna murnar ta ga mahaifin na ta, kuma shugaban kasar Najeriyar, Muhammadu Buhari. Ta dauki hoton ta tare da baban na ta, ta daura a shafin ta na Facebook

Zahara Buhari tare da Baban Ta Muhammadu Buhari

Shugaban Kasar Najeriyar Muhammadu Buhari wanda ya dawo kasar ne a ranar Lahadin jiya watau 19 watan yau bayan ya shafe kwanaki 14 a hutun da ya tafi ranar 6 ga watan Yunin nan a birnin Landan. Shugaba Buharin ya sauka filin jirgin kasar na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja wajen karfe 5:33 na yammacin jiya Lahadin. Mutanen da suka masa maraba sun hada da Gwamnan jihar Zamfara, Gwamna Abdul Aziz Yari da kuma danuwan sa na Jihar Kogi, Yahaya Bello. Da ma wasu daga cikin majalisar zartarwar Kasar, hade da manyan jami’an gwamnati, da ‘yan majalisun tarayyar Kasar da kuma Hafsun sojojin kasar.

Shugaban Kasar Najeriyar ya zagaye wani faretin ban girma da sojojin fadar sa suka yi masa yayin dawowan na sa.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng