Jonathan yaki halarta taron PDP na Kudu maso Kudu

Jonathan yaki halarta taron PDP na Kudu maso Kudu

- Tsohon shugaban kasa Jonathan bai halarci taron PDp na kudu maso kudu ba

- Wannan ya faru ne sakamakon rashin jituwa dake faruwa tsakanin dattawan jam'iyyar da yara matasa

- PDP ta sha alwashin kwace kujerar shugaban kasa

Jonathan yaki halarta taron PDP na Kudu maso Kudu
Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Dakta Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa Jonathan yaki halarta taron PDP na kudu maso kudu wanda aka gudunar a ranar Lahadi, 14 ga watan mayu, wanda aka gudanar a garin Fatakwal.

Ba'a bada wani dalili na rashin zuwa tsahon shugaban kasan ba. Amma jaridar The Punch ta ruwaito cewa ana tsammanin yaki zuwa ne saboda akwai rashin jituwa a cikin jam'iyyar tsakananin wasu dattawan jam'iyyar da kuma wasu matasan yan siyasa na jam'iyyar.

An gudanar da taron ne a Obi Waliinternational conferance Center dake a Fatakwal, inda tsofaffin Gwamnoni da sabbi a karkashin jam'iiay duka suka halarci taron.

A taron, sabon mataimakin Ciyaman dinjam'iyyar na kasa, Emmanuel Ogiri, ya bayyana cewa jam'iyyar zata sake amshe kujerar shugaban kasa a shekarar 2019.

Ogiri ya bayyana cewa rashin jituwa dake tsakanin dattijan jam'iyyar da kuma sabbin jini za'a warware shi kafin babban taron zaben sabon shugaban jam'iyyar na kasa da za'a gudanar a ranar 21 ga watan Mayu na 2016 a babban birnin Jihar Rivers, Fatakwal.

Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike, ya sha alwashin cewa jam'iyyar zata samu nasara a zaben jihar Edo wanda za'a gudanar a wannan shekarar.

Ya kuma bayyana cewa Gwamnonin yankin da kuma dattawan yankin sun sha alwashin tabbatar da cewa yankin kudu maso kudu ya cigaba da kasancewa yankin da jamiyyar PDP ke tunkaho dashi.

Yace " Gwamnoni da dattijan yankin nan zasu tabbatar da cewa PDP ta cigaba da irike wannan yankin. Zamuyi aiki a matsayin yan gida daya wajen taimaka ma yan jam'iyyar mu domin ganin cewa sun ci zaben jihar Edo wanda za'ayi a watan Satumba.

Wike ya bayyana cewa za'a gudanar da taron a cikin nasara a ranar 21 ga watan Mayu na 2016 a garin Fatakwal.

kafin fara taron tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma shugaban marassa rinjaye a majalisar daddata, Goodwill Akpabio, ya bayyana cewa yan Najeriya sun fara kira ga jam'iyyar PDP ta dawo mulki.

A wani labarain kuma, wasu yan jam'iyyar PDP sun fara zargin gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti akan kawo rudani cikin jam'iyyar a gaba da taron yan jam'iyyar da za'a gudanar, na yankin kudu maso yammacin Najeriya. Sun zarge shi da hakanne bayan da suka bayyana cewa yaci gaba da shirya taron wanda ake sanya rai za'a gudanara a Akure, babban birnin jihar Ondo. Sun bayyana cewa Fayose na kin bin umurnin kotu bayan data dakatar da gudanar da taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: