Jerin Jami'o'i 11 cikin 202 da Farfsesoshi Mata ke jagoranta a Najeriya

Jerin Jami'o'i 11 cikin 202 da Farfsesoshi Mata ke jagoranta a Najeriya

Har yanzu da sauran rina a kaba wajen samun daidaito tsakanin maza da mata wajen rike mukaman shugabanci a sashen ilimi da siyasa a Najeriya.

Bisa bayanan dake shafin yanar gicon hukumar Jami'o'in Najeriya NUC, an gano cewa cikin jami'o'i 202 dake Najeriya, 11 kadai mata ke jagoranta, TheCable ta tattaro.

Yayinda majalisar jami'a da gwamnonin jihohi ke nada shugabannin jami'a a jami'o'in gwamnati, mamallaki ke da hakkin nadawa a jami'o'i masu zaman kansu.

Jerin Jami'o'i 11 cikin 202 da Farfsesoshi Mata ke jagoranta a Najeriya
Jerin Jami'o'i 11 cikin 202 da Farfsesoshi Mata ke jagoranta a Najeriya Hoto: The Cable
Source: UGC

Ga jerin matan da ke jagorantar jami'o'i 11 da jami'o'in da suke jagoranta:

Read also

Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

1. Farfesa Lilian Salami - Jami'ar Benin

2. Farfesa Florence Obi - Jami'ar Calabar

3. Farfesa Achilike Akah - Jami'ar jihar Imo

4. Farfesa Chinedum Babalola - Jami'ar Chrisland

5. Farfesa Elisabeta Olarinde - Jami'ar Afe Babalola

6. Farfesa Nnenna Oti - Jami'ar Fasaha ta tarraya Owerri (FUTO)

7. Farfesa. Ibiyemi Olatunji-Bello - Jami'ar jihar Legas (LASU)

8. Kaletapwa G Farauta - Jami'ar jihar Adamawa

9. Farfesa Ibiyinka Fuwape - Jami'ar Michael/Cecilia Ibru

10. Farfesa Margee Ensign - Jami'ar American ta Nigeria, Yola

11. Farfesa Adenike Kuku - Jami'ar Kings Odeomu, Osun

Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki, Ta Fadi Dalili

Malaman jami'o'i ka iya komawa yajin aiki bayan gwamnatin tarayya da gaza cika yarjejeniyar da ta cimmawa da ƙungiyar ASUU, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Shugaban ƙungiyar reshen jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, Bauchi (ATBU), Ibrahim Inuwa, yace:

Read also

Hare-haren ta’addanci: Birtaniya ta gargadi 'yan kasarta akan zuwa wadannan jihohi 12 na Najeriya

"Cikin yarjejeniya takwas da aka amince da su a baya, biyu kacal gwamnatin tarayya da cika musu."

Inuwa ya bayyana cewa sauran shida da gwamnati ta gaza aiwatarwa sun haɗa da biyan alawus ɗin malaman jami'a, samar da kuɗaɗe domin farfaɗo da jami'o'i, ƙara yawan jami'o'in jiha, sake zama teburin shawarwari da kuma maye tsarin biyan albashi IPPIS da wanda ASUU ta gabatar UTAS.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel