Badakalar fili: Sheikh Kalarawy ya ajiye mukaminsa saboda za a gina shaguna a masallacin idi

Badakalar fili: Sheikh Kalarawy ya ajiye mukaminsa saboda za a gina shaguna a masallacin idi

  • Fitaccen Malamin musulunci a jihar Kano ya ajiye mukaminsa a masallacin Fagge
  • Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya yi hakan saboda batun gina shaguna a masallacin
  • ‘Yan majalisar dokokin Kano sun tsoma bakinsu a lamarin, za a binciki badakalar

Kano - Da jin babban malamin nan, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya bada sanarwar yin murabus daga kwamitin masallacin Fagge, majalisa ta shiga maganar.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, 2021, cewa ‘yan majalisar dokokin jihar Kano sun hana a gina shaguna jikin masallacin Juma’an.

Wani mataki 'Yan majalisa suka dauka?

Shugaban majalisar dokoki na jihar Kano, Rt. Hon. Hamisu Ibrahim Chidari ya yi magana a dazu, ya bada umarnin a dakatar da gine-gine a harabar masallacin.

Read also

Yanzu-yanzu: Bayan tirka-tirka, an zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Kontagora

Honarabul Hamisu Ibrahim Chidari ya kuma kafa wani kwamitin mutum tara da zai duba lamarin.

‘Yan majalisar sun dauki wannan mataki ne a sakamakon korafin da ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Dala, Hon. Lawan Hussaini ya kawo a zaman yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masallacin idi
Gwamna, Mataimakinsa da Sarkin Kano a masallaci Hoto: www.solacebase.com
Source: UGC

Hon. Lawan Hussaini yake cewa abin da ya faru da masallacin na Fagge, babban abin takaici ne. Hakan ya jawo aka yi ta muhawara a zauren majalisar jihar.

Muhammad Uba Gurjiya mai wakiltar Bunkure ne zai jagoranci wannan kwamiti tare da Sunusi Usman Bataiya, Magaji Dahiru Zarewa, da dhi Lawan Hussaini.

Sauran ‘yan kwamitin sune: Nuhu Abdullahi Achika, Abubakar Dalladi Isa Kademi, Muhammad Tukur da Sale Marke, sai wani jami’i a matsayin sakatarensu.

Badakalar filaye a Kano

Jaridar tace an dade ana samun badakalar filaye irin wannan a jihar Kano a ‘yan shekarun bayan nan.

Read also

Da dumi-dumi: Allah ya yi wa Sanata Abdulazeez, kanin Mama Taraba, rasuwa

Kamar yadda Kano Focus ta fitar da rahoto, Sheikh Kalarawi ya sauka daga mukamin da ya dade a kai bayan jin an bada filin masallaci domin ayi wasu shaguna.

Boko Haram a Neja?

A makon nan ne aka samu rahoto cewa ‘Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun auka wa wasu kauyukan jihar Neja, sun kayyade wa ‘Yan mata shekarun aure.

Tun tuni aka ji Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello yana cewa ba da ‘Yan bindiga suke yaki a jihar ba, sojojin Boko Haram ne suka shigo yankin, suna yin ta'adi.

Source: Legit.ng

Online view pixel