Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar NECA, Timothy Olawale, ya mutu a Abuja

Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar NECA, Timothy Olawale, ya mutu a Abuja

  • Shugaba Buhari yayi rashin daya daga cikin wadanda ya ba mukami 2019
  • Dr Timothy ya mutu ne bayan rashin lafiya a birnin tarayya
  • Kungiyar NECA tayi alhinin rashinsa

Legas - Dirakta Janar na hukumar bada shawara ga masu daukan aiki (NECA) Dr Timothy Olawale ya rigamu gidan gaskiya, kungiyar ta bayyana.

Sakatariyar hukumar dake Legas ta bada sanarwa ne ranar Asabar cewa Olawale ya mutu ranar Juma'a, 1 ga Oktoba, a wani asibitin Abuja, rahoton Tribune.

A jawabin, Olawale ya bar matarsa guda da 'yaya.

Jawabin yace:

"Da alhini muke sanar da mutuwar Dr Timothy Olawale, dirakta janar dinmu, wanda ya mutu ranar 1 ga Oktoba, 2021 a wani asibitin Abuja."
"Ya bar matarsa, yara da sauran yan uwa; muna addu'a Allah ya kara musu hakurin wannan babban rashi."

Read also

Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha

An tabbatar Dr Timothy matsayin Shugaban NECA a Junairun 2019 bayan watanni shida yana mukaddashi.

Yanzu-yanzu: Shugaban kungiyar NECA, Timothy Olawale, ya mutu a Abuja
Yanzu-yanzu: Shugaban kungiyar NECA, Timothy Olawale, ya mutu a Abuja Hoto: Nigeria Tribune
Source: UGC

Tsohon gwamnan Najeriya ya mutu a ranar bikin samun 'yancin kai

A daidai lokacin da 'yan Najeriya suke bikin murnar ranar yancin kan kasarsu, sai ga wani labari mara dadi na wani mutuwa da ya zo a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba.

Kamar yadda AIT News ta ruwaito, tsohon gwamnan na Cross River da Delta a mulkin soji, Commodore Ibrahim Kefas (mai ritaya), ya rasu a ranar Juma'a a wani asibitin Abuja yana da shekaru 73.

An binne marigayin daidai da koyarwar addinin Islama a wannan ranar.

Marigayi Kefas ya yi gwamnan soja na jihohin biyu tsakanin 1993 zuwa 1996 a zamanin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha.

Source: Legit.ng

Online view pixel