Hotunan 'yan majalisar wakilan arewa a ziyarar da suka kai wa Tinubu birnin London

Hotunan 'yan majalisar wakilan arewa a ziyarar da suka kai wa Tinubu birnin London

  • 'Yan majalisar wakilan Najeriya na arewaci sun ziyarci Bola Tinubu a London
  • An gano cewa 'yan majalisar sun je duba karfin jikin jigon APC bayan an yi masa aiki
  • A kwanakin baya, gwamonin kudu sun kai wa tsohon gwamnan jihar Legas ziyara

London - 'Yan majalisar wakilan Najeriya na arewacin kasar nan sun samu jagorancin mataimakin kakakin majalisa, Ahmed Idris Wase inda suka ziyarci jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a London ranar cikar Najeriya shekaru sittin da daya da samun 'yancin kai.

Daily Trust ta tattaro cewa, majiya daga ofishin jam'iyya mai mulki ta kasa ta ce 'yan majalisar wakilan sun tattaro daga arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu

Hotunan 'yan majalisar wakilan arewa a ziyarar da suka kai wa Tinubu birnin London
Hotunan 'yan majalisar wakilan arewa a ziyarar da suka kai wa Tinubu birnin London. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi tun a baya sun ziyarci tsohon gwamnan jihar Legas a London.

An gano cewa, an yi wa Tinubu aiki a London, inda yanzu haka ya ke jinya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daraktan yada labarai da hulda da jama'a na kungiyar goyon bayan Tinubu, Tosin Adeyanju, ta tabbatar wa da Daily Trust cewa 'yan majalisar wakilan sun ziyarci Tinubu a London.

Hotunan 'yan majalisar wakilan arewa a ziyarar da suka kai wa Tinubu birnin London
Hotunan 'yan majalisar wakilan arewa a ziyarar da suka kai wa Tinubu birnin London. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng