‘Dan takara ya samu nasara a kan PDP, Alkali yace a dawo masa da N4.5m da ya biya a 2015

‘Dan takara ya samu nasara a kan PDP, Alkali yace a dawo masa da N4.5m da ya biya a 2015

  • Babban kotun daukaka kara ta yanke hukunci a shari’ar Chukwunweike Maduekwe
  • Abubakar Datti Yahaya ya umarci PDP ta dawo wa Maduekwe da kudin sayen fam
  • Barista Maduekwe ya saye fam din neman takarar Sanata a 2015, amma bai dace ba

Abuja - Babban kotun daukaka kara da ke zama a birnin tarayya Abuja, ta saurari karar Barista Chukwunweike Maduekwe da jam’iyyar PDP.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Chukwunweike Maduekwe ya samu nasara a karar da ya kai PDP, yana neman a dawo masa da kudinsa.

Barista Maduekwe ya saye fam yana sha'awar takarar Sanatan Anambra ta tsakiya a jam’iyyar PDP, amma yace ba a yi zaben fitar da gwani ba.

Rahoton yace Chukwunweike Maduekwe ya saye fam din neman takarar ne tun a zaben 2015.

Read also

Asirin fitattun ‘Yan siyasa da 'Yan kasuwan Najeriya 10 ya tonu a badakalar Pandora Papers

Maduekwe ya kai karar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC da Sanata Uche Ekwunife ta hannun babban lauya, Patrick Ikwueto SAN.

Kamfe a Delta
'Yan takarar PDP a Delta Hoto: punchng.com
Source: UGC

Patrick Ikwueto SAN ya gabatar wa kotu hujjoji da ke gamsar da ita cewa PDP ba ta gudanar da zaben cikin gida kafin a saida masa fam din ba.

Kotu ta ba Chukwunweike Maduekwe gaskiya

A ranar Alhamis, 30 ga watan Satumba, 2021, Alkali Abubakar Datti Yahaya da wasu Alkalai uku suka saurari shari’ar, suka zartar da hukunci.

Alkali mai shari’a Abubakar Datti Yahaya ya bukaci jam’iyyar PDP ta maida wa Chukwunweike Maduekwe kudin da ya bada wajen mallakar fam.

Da wannan hukunci da aka yi, PDP za ta dawo wa Maduekwe da Naira miliyan 4.5 da ya bada domin sayen fam din sha’awa da shiga takara.

Read also

An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya rasu a hannun 'yan bindiga

PDP da lissafin 2023

Bisa dukkan alamu jam’iyyar PDP tana shirin watsi da ‘Yan siyasan Arewa a takarar shugaban kasa, inda aka ba yankin kujerar shugaban jam'iyya.

Idan aka tafi a haka, babu mamaki ‘Dan Kudu zai rike wa PDP tuta a zaben 2023. Sai dai idan kwamitin Ifeanyi Ugwuanyi ya bar takarar a bude.

Source: Legit.ng

Online view pixel