Yan sandan Saudiyya sun damke dan Masar ya taba wata mata a wurin da bai dace ba
- An damke wani matashi da ya cin zarafin mace cikin jama'a
- A bidiyon da ya bayyana a TikTok, mutane sun damkeshi kai tsaye
- Wannan laifi babba ne a hukuncin dokokin kasar Saudiyya
Saudiyya - Jami'an yan sandan Jeddah sun damke wani dan kasar Masar kan laifin taba wata mata a bainar jama'a a wurin da bai dace ba kuma ba tare da izininta ba.
A wani bidiyon Tiktok da ya bayyana, an ga mutumin yana taba matar a wajen zama kuma hakan ya sabawa dokokin cin zarafin na 2018.
Ukubar da doka ta tanada wa irin wannan laifi na iya kaiwa zaman Kurkuku na shekaru biyu da kuma tarar Riyal 100,000.
Idan kuma cin zarafin kananan yara ne, za'a iya daure mutum shekaru biyar a gidan yari da tarar Riyal 300,000.
Sakamakon kafa wannan dokar, an samu raguwar laifin cin zarafi a Saudiyya, cewar 'Saudi Gazette'.
Kalli bidiyon:
Karon farko, Hotunan Mata sun yi fareti a bikin tunawa da ranar Saudiyya
Karon farko a tarihin Kasar Saudiyya, mata a kasar Saudiyya sun yi musharaka a bikin tunawa da ranar kafa kasar ta Saudiyya.
Ana murnar ranar Saudiyya ne kowace 23 ga Satumba shekara domin murnar ranar da aka canza sunan kasar daga Masarautar Najd da Hijaz zuwa Masarautar Saudiyya.
Asali: Legit.ng