Babu wanda ya kai ni sa'a a duniya: Shugaban masu shara da tsaftace Masallacin Ka'aba, Ahmed Khan
- Shugaban masu shara a Masallacin Harami ya bayyana irin farin cikin da yake yi
- Dattijon ya shiga Saudiyya yana matashi har ya manyanta yanzu
- Mutumin ya kwashe shekaru 40 yana tsaftace Masallacin Ka'aba
Saudiyya - Wani dan kasar Pakistan wanda ya je kasar Saudiya neman aiki tun 1983 ya zama Shugaban masu aikin tsaftace Masallacin Ka'aba mafi daraja a Musulunci.
Ahmed Khan ya shiga Saudiyya yana dan shekara 23 lokacin mulkin marigayin tsohon Sarkin Saudiyya, Fahd bin Abdul Aziz.
Shafin 'Life in Saudi Arbabia' ta bayyana cewa tun daga lokacin yake aikin sharan Masallacin Ka'aba har yanzu.
Yayinda ya kai shekaru 61, ya zama Shugaban masu shara da tsaftace Masallacin.
Ahmad Khan ya bayyana cewa yana ganin kansa a matsayin mutum mafi sa'a a duniya.
Yace:
"Ina zaune a wurin da mutane ke kashe dubunnan daloli don zuwa na mako daya kacal."
"Za ka samu farin ciki, kwanciyan hankali, rahama da natsuwa a dukkan sassan Masallacin Harama."
Tsohon Saurayin Amarya ya aikewa sabon angonta hotunanta na lalata, aure ya mutu a daren farko
A wani labarin daban, a daren farko ya mutu yayinda ake tsakiyar shagalin biki lokacin da Ango ya smau sakon hotunan Amaryarsa na irin lalatan da tayi a shekarun baya kafin su hadu.
Shafin LISA ya ruwaito cewa ngon ya samu wasika tattare da katin Memory da wani ya turo yana zargin Amaryar da kasance mutuniyar banza.
Hakan ya sa Angon ya hanzarta wajen kallon abinda ke cikin Memorin.
Asali: Legit.ng