Zamu katse layukan sadarwa a jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufa'i

Zamu katse layukan sadarwa a jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufa'i

  • Jihar Kaduna za ta shiga jerin jihohin da aka kaste layukan sadarwa
  • Jihar Kaduna tuni na fama da matsalar yan bindiga masu garkuwa da mutane
  • Jihar Zamfara, Sokoto, da Kastina tuni sun dau wannan mataki

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya sanar da al'ummar jiharsa cewa su shirya za'a kaste layukan sadarwarsu saboda ana shirin afkawa yan bindiga dake boye a wasu kananan hukumomin jihar.

El-Rufai yace wannan abu da za'a yi ba zai shafi dukkan jihar ba, wasu kananan hukumomi masu makwabtaka da Zamfara da Katsina inda Sojoji ke aiki zai shafa.

Jawabi yayin hira da gidajen rediyon jihar a daren Talata, El Rufa'i yace sun nemi izini wajen Shugaba Buhari kuma ya basu dama, rahoton DailyTrust.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

A cewarsa:

"Sojoji da jami'an tsaro sun bamu shawara cewa mu datse layukan sadarwa a wasu kananan hukumomi amma muna sauraransu su fada mana lokacin da zasuyi da kuma wuraren."
"Amma ina son mutan Kaduna sun sani cewa idan aka bamu dama gobe, zamu katse layukan gobe."

El-Rufa'i yace sakamakon katse layukan sadarwan da akayi a Katsina da Zamfara, rahotanni sun nuna cewa yan bindigan sun fara guduwa Kaduna domin kiran iyalan wadanda suka sace don karban kudin fansa.

Zamu katse layukan sadarwa a jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufa'i
Zamu katse layukan sadarwa a jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufa'i Hoto: Governor of Kaduna
Source: UGC

Buhari ya amince mu katse layukan

Gwamnan yace tuni ya aikewa gwamnatin tarayya wasika kan hakan kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da hakan.

Hakazalika yace ba zai bayyana kananan hukumomin da abin zai shafa ba. Yace idan lokacin yayi, za'a sanar.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Yace:

"Ba zan sanar da kananan hukumomin da abin zai shafa ba amma wadanda yan bindiga suka addaba sun san kansu."
"Hukumomin tsaro na cewa lokaci yayi da zamu sanar da al'ummar Kaduna."

A makonnin baya-bayan nan, Legit ta fahimci kananan hukumomin da yan bindiga suka addaba a jihar Kaduna sun hada da Birnin Gwari, Giwa, Chikun, da Kaura.

Source: Legit

Online view pixel