Gwamnatin Tarayya na bin kamfanonin mai bashin Naira tiriliyan 2.7, za a hada da EFCC

Gwamnatin Tarayya na bin kamfanonin mai bashin Naira tiriliyan 2.7, za a hada da EFCC

  • Hukumar NEITI tace gwamnati na bin kamfanonin mai bashin makudan kudi
  • Shugaban NEITI yace akwai bashin kusan Naira tiriliyan 2.7 kan kamfanoni 77
  • Orji Ogbonnaya-Orji yayi barazanar hada-kai da EFCC domin a iya karbo kudin

Abuja - Bashin da gwamnatin tarayya ta ke bin wasu kamfanonin mai ya kai Naira tiriliyan 2.66. Shugaban hukumar NEITI na kasa ya bayyana wannan.

Jaridar Punch ta rahoto Orji Ogbonnaya-Orji yana cewa gwamnatin kasar na bin kamfanonin mai 77 bashin kudi daga harajin da ya kamata a ce suna biya.

An kuma rahoto Orji Ogbonnaya-Orji yana cewa NEITI za ta wallafa sunayen wadanda suka ki sauke nauyin da ke kansu, sannan za a hada su da EFCC.

Ogbonnaya-Orji yace bashin da suke kan wadannan kamfanonin sun taru ne daga harajin da ake karba daga riba, bunkasa ilmi, kudin shiga da dai sauransu.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Kamar yadda muka samu labari a ranar Talatar, shugaban hukumar ta NEITI yace an tattaro wadannan bashi daga binciken kudin da aka yi a 2019.

Shugaban NEITI
Shugaban NEITI, Dr. Orji Ogbonnaya-Orji Hoto:@DrOrjiOOrji
Source: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda aka tara bashin N26tr

“Rahoton NEITI ya tabbatar da cewa sakamakon binciken da aka yi na mai a 2019 ya nuna kamfanonin mai da gas a Najeriya suna da bashin $6.48bn.”
“Wannan kudi ya kai Naira tiriliyan 2.66 a yadda ake canjin Dalar Amurka yau a kan N410.35.”
“An samu $143.99m daga harajin ribar fetur, $1.089bn a harajin kudin shiga, da $201.69m a harajin ilmi.”
“Sauran bashin da suka taru sun hada da $18.46m da £972,000 a VAT. An bada sauran kason da $23.91m da £997,000, sai $4.357bn da $292.44m.”
“Har ila yau akwai tarar $270.187m da $41.86m da aka lafta wa wasu cikin wadannan kamfanonin mai da suka saba doka da ka’idar aiki a Najeriya.”

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Za a fara aikin wutan Mambilla

A makon nan aka ji Sanata Teslim Folarin yana cewa an shawo kan tirka-tirkar kotu ta sa aka gagara soma kwangilar lantarkin Mambilla bayan shekaru biyu.

Sanata Teslim Folarin yana sa rai nan da ‘yan watanni a ga ayyuka sun fara kankama a Taraba.

Source: Legit

Online view pixel