Tsohon shugaban 'yan sanda a Kenya ya naushi lauya a kotu saboda damunsa da tambayoyi yayin shari'a

Tsohon shugaban 'yan sanda a Kenya ya naushi lauya a kotu saboda damunsa da tambayoyi yayin shari'a

  • Tsohon darektan ayyukan ‘yan sandan kasar Kenya, John Edward Njeru ya naushi lauya a kotu bayan ya dame shi da tambayoyi
  • Sanadiyyar hakan lauyan, Alex Kimani ya samu mummunan rauni a cikin sa daga nan alkalin ya bukaci a rike shi kuma a sanar da ‘yan sanda don bincike
  • Kamar yadda bayanai suka kammala, ya hassala ne sakamakon tambayoyin kurar halin da lauyan ya yi ta ma sa duk da shaida ya je yi kotun

Kasar Kenya - Tsohon darektan ayyukan ‘yan sanda, ya naushi lauya a kotu sakamakon yadda ya taso shi da tambayoyi yayin da ake shari’a a kotun kasar Kenya.

Sakamakon hakan, alkalin ya bukaci tsohon mai shekaru 69, John Edward Njeru ya kwana 1 a gidan gyaran hali sakamakon cin zarafin lauya a cikin kotu kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Tsohon shugaban 'yan sanda a Kenya ya naushi lauya a kotu saboda damunsa da tambayoyi yayin shari'a
Tsohon direktan ayyukan 'yan sanda a Kenya, John Edward a Kotu. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Tsohon darektan ayyukan ‘yan sandan Kenyan ya bar lauyan, Alex Kimani da munanan raunuka a cikin sa. Ya fusata akan yadda Kimani ya ta sa shi da tambayoyi bayan ya je shaida a kotun.

Njeru ya je shaida ne a kotun

Ana hukunci ne tsakanin wani dattijo wanda ya zargi wani dan kasuwa, Gabriel Njoroge Mbuthia da yin takardar fili ta bogi a anguwar Nanyuki. Ana zargin dan kasuwar da aikata laifin a ranar 21 ga watan Yulin 2009.

Kamar yadda LIB ta ruwaito lamarin ya faru ne bayan lauyan ya bukaci kotu ta bar shaidar ya matso kusa da shi don ya bayyana masa wasu takardu. An nemi kotun ta rike shaidar saboda lauyan da yake shari’ar ya je asibiti don duba lafiyar sa.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Kimani ya je asibiti duba lafiyarsa saboda naushin da ya sha

Abokin aikin sa, Waweru Benson wanda ya bayyana gaban kotu a ranar 28 ga watan Satumba ya sanar da mai gabatar da shari’ar Bernard Ochoi cewa Kimani ba zai samu damar zuwa kotu ba saboda ciwon ciki da yake damun sa.

Kamar yadda Benson ya ce:

“Bayan aukuwar lamarin jiya, abokin aiki na, Kimani ya fuskanci matsanancin ciwo a cikin sa. Ya nufi asibiti kuma likita ya shawarce shi da ya je a bincika ainihin abinda yake damun sa da na’urar asibiti.”

Benson ya bukaci kotu ta hada kai wurin kawo karshen rashin cin zarafi morning irin wannan kuma ya bukaci kotu ta rike Njeru ya kara kwanaki har sai an sanar da ‘yan sanda abinda ya faru.

Alkalin kotun ya ce:

“Bayan aukuwar mummunan lamarin da ya faru jiya wanda shaida ya naushi lauya, na umarci a rike shaidar na kwana daya. An sanar da ni yadda lauyan ya ke fama da rashin lafiya sakamakon lamarin kuma muna bukatar ya yi gaggawar sanar da ‘yan sanda don su yi bincike akan lamarin kuma su turo korafin zuwa kotu.”
“Kotu ba za ta amince da irin wannan lamarin ba kuma ta yi alawadai da faruwar hakan.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel