Da duminsa: Ganduje ya nada Alhaji Aliyu Ibrahim, sabon Sarkin Gaya

Da duminsa: Ganduje ya nada Alhaji Aliyu Ibrahim, sabon Sarkin Gaya

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a matsayin sabon sarkin masarautar Gaya.

Wannan ya biyo bayan zabinsa da masu zaben Sarkin masarautar sukayi.

Sakataren Gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya bayar da wannan sanarwa a gidan gwamnatin jihar yayinda aka karbi bakuncin masu zaben Sarki.

Da duminsa: Ganduje ya nada Alhaji Aliyu Ibrahim, sabon Sarkin Gaya
Da duminsa: Ganduje ya nada Alhaji Aliyu Ibrahim, sabon Sarkin Gaya Hoto: Ganduje TV
Asali: Facebook

Rasuwar Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim AbdulKadir

A Laraba, 22 ga Satumba 2021, Allah ya yiwa Mai Martaba Sarkin Gaya , Alhaji Ibrahim AbdulKadir, rasuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin babban hadimin gwamnan Kano kan kafafen yada labaran zamani, Abubakar Aminu Ibrahim.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan mako daya a Amurka, Buhari na kan hanyarsa ta dawowa gida Najeriya

Sarkin ya rasu yana mai shekaru 91 a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel