Jigogin PDP sun gindaya sharudan da wanda zai zama Shugaban Jam’iyya zai cika

Jigogin PDP sun gindaya sharudan da wanda zai zama Shugaban Jam’iyya zai cika

  • Wasu tsofaffin shugabannin PDP sun yi magana game da zabe mai zuwa
  • Jagororin jam’iyyar suna so a zakulo shugabanni masu nagarta ne a PDP
  • Dr. Kema Chikwe da Barista Mark Jacob sun fitar da jawabi a makon nan

Abuja – Wasu tsofaffin shugabannin PDP sun bada wasu ka’idojin zama sabon shugaban jam’iyyar adawar.

Wadannan mutane da suka rike mukami a majalisar NWC na jam’iyyar PDP a baya sun ce sai sabon shugaban jam’iyyar ya zama mai wadannan halaye.

Jaridar Daily Trust tace ‘ya ‘yan jam’iyyar sun fada wa majalisar amintattu ta BOT da kungiyar gwamnonin PDP cewa a kawo shugaban da ba za a juya ba.

Kungiyar tsofaffin shugabannin ba su san wanda bai da ta-cewar kansa ya karbi ragamar PDP.

Haka zalika ‘yan jam’iyyar suna so duk wanda zai rike kujerar shugaban jam’iyyar PDP na kasa ko sakatare ya zama mutum ne da aka yarda da nagartarsa.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Jigogin PDP
'Yan Jam’iyyar PDP suna taro Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana ganin gwamnonin jam'iyya, majalisar BOT da 'yan majalisa suna da rawar da za su taka wajen fito da sababbin shugabannin jam'iyyar PDP na kasa.

Rahoton yace tsofaffin jagororin jam’iyyar sun fitar da wannan jawabi ne ta bakin shugaban kungiyarsu, Dr. Kema Chikwe da sakatarensa, Mark Jacob.

A jawabin na su, Dr. Kema Chikwe da Barr. Mark Jacob sun ce ana bukatar a samu shugabannin da ake ganin su da daraja da kuma kima a jam’iyyar adawar.

Haka zalika ana so shugabannin su zama wanda ‘yan Najeriya da kasashen Duniya suka yaba da halinsu.

Kema Chikwe bai yi wa kowa mubaya’a ba, sannan kuma bai nuna wanda suke goyon baya a zaben shugaban jam’iyya ko kuma sakataren PDP na kasa ba.

Jega sun fito da sabuwar tafiyar siyasa

A makon nan ne Farfesa Attahiru Jega ya bada shawarar cewa ya kamata a soke wasu Jihohin kasar nan, a koma tsarin Gwamnoni 12 da ake kai a 1976/1977.

Kara karanta wannan

APC ta gindaya wa FFK sharuddan da zai cika kafin ta gama amincewa da shi

Maimakon kara yawan jihohi su kai 42, Farfesa Jega yana so jihohin Najeriya su zama 12. Jega ya bayyana haka lokacin da suka kafa wata sabuwar tafiyar siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng