Alherin danko ne: Hadisai 9 daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Alherin danko ne: Hadisai 9 daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malam ya yi bayani kan muhimmancin yin alheri .

NA FARKO (1)

Manzon Allah (saw) Yace:-

"Duk Wanda Ya kasance Cikin Biyan Buqatar Dan Uwansa, Allah Zai Kasance Cikin Biyan Buqatar Sa."

(Sahih Jami'i)

NA BIYU (2)

Manzon Allah (saw) Yace:

"Allah Yana Cikin Taimakon Bãwa, Matuqar Bãwa Yana Taimakon Dan Uwansa"

(Muslim ya ruwaito)

NA UKU (3)

Manzon Allah (saw) Yace:

"Wallahi In Kasance Cikin Biyan Buqatar Dan Uwana Musulmi, Yafi Soyuwa Agareni Akan Inyi E'itikhãfi Na Wata Daya A Masallaci"

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa Matar Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, gwamnan Bauchi yayi ta'aziyya

(Silsilatul Sahiha)

NA HUDU (4)

Manzon Allah (saw) Yace:

"Duk Wanda Ya Tafi Tare da Dan Uwansa Musulmi Cikin Biyan Buqatar Sa, Har ya Tabbatar Masa Da Buqatar Sa, Allah Zai Tabbatar da Diddigen Sa Ranar da Digadigai Zasu Zame (Akan Siradi)"

(Silsilatul Sahiha)

Alherin danko ne: Hadisai 9 daga Sheikh Aminu Ibrahim Daura Kano
Alherin danko ne: Hadisai 9 daga Sheikh Aminu Ibrahim Daura Kano Hoto: Mal.Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

NA BIYAR (5)

Manzon Allah (saw) Yace:

"Mafificin Aiki Acikin Ayyuka Shine: Ka Sanya Farin Ciki ga Dan Uwanka Mumini, Ko Ka Biya Masa Bashin da Ake Binsa, Ko Ka Ciyar dashi Abinci"

(Sahihul Jami'i)

NA SHIDA (6)

Manzon Allah (saw) Yace:

"Duk Wanda Ya Sauqaqa Ma Wanda Yake Cikin Qunci, Allah Zai Sauqaqa Masa Acikin Duniya da Lahira."

(Sahihul Jami'i)

NA BAKWAI (7)

Manzon Allah (saw) Yace:

"Duk Wanda Yake Son Allah Ya Tseratar dashi daga Quncin Ranar Alqiyamah, To ya Yaye Damuwar Wanda Yake Cikin Tsanani."

(Muslim ya ruwaito)

NA TAKWAS (8)-

IBNUL QAYYIM (RH) YACE:

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon mataimakin gwamnan CBN da ya rasu

Lallai Acikin Biyan Buqatun Mutane Akwai Wani Dandano, da Babu Wanda Yasanshi Sai Wanda Ya Jarraba.

Ka Aikata Alkari ga Mutane Duk Yadda Kake Ganin Qanqantar Sa,

Domin Baka San Wani Aikine Zai Shigar Dakai Aljannah ba.

NA TARA (9)

Manzon Allah (saw) yace:

"Mafi Alkairi Daga Cikin Mutane, Shine Wanda Mutane Ke Amfanuwa Dashi."

(Bukhari da Muslim)

.

Yaa Allah Kasa Mu Zamto Alkairi ga Mutane, Ba Sharri A Garesu ba.

#Fatan_Alkairi

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng