Gwamna Ortom: An yi min tayin APC, gwamnatin Buhari ba ta taimaka min wurin biyan albashi

Gwamna Ortom: An yi min tayin APC, gwamnatin Buhari ba ta taimaka min wurin biyan albashi

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya zargi gwamnatin tarayya da rashin taimako a gare shi
  • Ya ce akwai wadanda suka tallata ma sa shiga jam’iyya mai mulki ta APC amma ya ki shiga saboda mutanen sa
  • A cewar sa yanzu haka gwamnatin tarayya ba ta tallafa masa wurin biyan albashi da fansho

Jihar Binuwai - Gwamnan jihar Binuwai, Mr Samuel Ortom ya jefi gwamnatin tarayya da wani zargi kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

A cewar Ortom, gwamnatin tarayya tana tura kudi mara yawa ga gwamnatin jihar sa don haka ba ya samun damar biyan albashin ma’aikatan sa yadda ya dace.

Gwamna Ortom: An yi min tayin APC, gwamnatin Buhari ba ta taimaka min wurin biyan albashi
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ortom ya ce an yi masa tallar APC

Kara karanta wannan

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

Ya kara da bayyana yadda wasu mutane suka je har inda yake inda suka bukaci ya canja shekar sa ya koma APC, inda ya kara da cewa ba ya samun tallafin da ya dace daga gwamnatin Muhammadu Buhari kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Ya kara bayyana cewa naira biliyan 28 da gwamnatin tarayya ta ba shi be ishe shi biyan bashin naira biliyan 70 ba, inda ya kwatanta da sauran kudaden da ake bai wa wasu jihohi.

Kamar yadda Ortom ya bayyana:

“An dade ana cutar dani ana so ayi amfani da wata dama a kai na. Ina yi wa kasar nan fatan alheri shiyasa ake ganin ina amfani da kalolin sutturun wasu yaruke na jihar Binuwai; kamar Tibi, Idoma, Egede ba kalar tutar Najeriya ba. Na yi imani da Najeriya. Karfin mu shi ne hadin kan mu. Kuma na yarda zamu iya taruwa mu yi aiki gabadaya.

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

“Gwamnatin tarayya ta ki taimakamin wurin biyan kudaden fansho da garatuti wanda na gada daga gwamnatin baya. Ba laifi na bane. Aper Aku ya gaji bashin albashi da garatuti, Adasu ma haka, Suswam ma ya gada gashi nima na gada. Na gaji bashin naira biliyan 70 na kudin fansho, albashi da garatuti. Kuma ba sabon abu bane.
“Gwamnatin tarayya ta bani naira biliyan 28 kuma na yi amfani dasu sai dai bai isa ba. Wasu sun samu amma gwamnati ta ki tallafa min in karasa biyan sauran.
“Mutane sun zo suna ce min idan na koma APC, zasu mara min baya na ce ba zan iya bai wa mutane na kunya ba. Sun zabe ni, bazan so abinda zai sosa musu rai ba kuma matsawar su na baya na zan cigaba da jajircewa akan su. Idan su ka juya min baya ina kake so in je?”
“Ba wai na tsani Fulani bane kawai na tsani karya doka ne. Nan jihar Binuwai bana matsa wa kowa. Na bar kiristoci su yi addinin su haka zalika musulmai ko ma marasa addini. Kowa zai iya yin abinda yake so.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel