IBB: Shonekan yana 1 daga cikin hazikan da suka tafiyar da gwamnatina

IBB: Shonekan yana 1 daga cikin hazikan da suka tafiyar da gwamnatina

  • Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya kwantanta marigayi Shonekan da daya daga cikin hazikan da suka tafiyar da gwamnatinsa
  • A cewar Babangida, ya shiga alhini da jimami tun bayan samun labarin mutuwar Shonekan wanda bai yi tsammanin zai bar duniya yanzu ba
  • Babangida ya bayyana yadda Shonekan ya kasance mai kishin kasa kuma masani a fannin tattalin arziki da hanyoyin raya kasa

Minna, Niger - Tsohon shugaban kasan mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), ya kwatanta marigayi Chief Ernest Shonekan a matsayin daya daga cikin masu hangen nesa a lokacinsa.

Shonekan ya amsa mulki daga Babangida a 26 ga watan Augusta, 1993, yayin da janar Sani Abacha ya ture gwamnatin sa a ranar 17 ga Nuwamba, 1993.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya bada umurnin rage tsayin tutar Najeriya sakamakon mutuwar Ernest Shonekan

Shonekan yayi 'mutuwar Allah da annabi' ne inji iyalansa, Daily Trust ta ruwaito hakan.

IBB: Shonekan yana 1 daga cikin hazikan da suka tafiyar da gwamnatina
IBB: Shonekan yana 1 daga cikin hazikan da suka tafiyar da gwamnatina. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wata takarda da ya fitar a ranar talata, Babangida ya siffanta mutuwar Shonekan da babban rashi ga Najeriya.

Takardar ta ce:

"Labarin mutuwar daya daga cikin hazikai kuma masu kishin kasa ya riskeni a safiyar yau yayin da ya sakani cikin jimami da alhini. Ban taba tsammanin Chief Ernest Shonekan zai yi kaura daga duniyar nan da wuri haka ba, duk da shekararsa 85.
"Shi gwarzon namiji ne, shugaba sannan ba kamar kowa ba wurin kishin kasa wanda yake da hangen nesa da fahimtar Najeriya kuma abin alfahari. Tabbas wannan rashin nawa ne karan kaina.
"A lokacin rayuwarsa, shi ne mai tsara mana yadda tattalin arzirki ya kamata ya kasance wanda ke taimakawa wajen karfafa bangarori masu zaman kansu. Hangen nesa game da tattalin arzirki, hannayen jari da bunkasa bangaren."

Kara karanta wannan

Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa

Daily Trust ta ruwaito cewa, ta kara da cewa:

"Noma da kiwo da tsarin kasafi duk bakomai bane a lissafi da basirarsa.
"Bayan lissafa cigaban da ya kawo a lokacin muna kan karagar mulki a bangaren ababen more rayuwa, tattalin arzirki da dawowar wayewa, ya cancanci godiya daga garemu na amfani da hazakarsa don warware mana zare da abawa.
"Ya zama jigon mulkinmu duk lokacin da muka nemi agajinsa. Shi mutum ne mai bada himma wanda kishin kasarsa baya misaltuwa.
"Mutum ne wayayye kuma mai fara'a. Wanda ya san tattalin arzirki kuma yayi hangen nesa da dama, hakan ya taimaka wajen fidda kasar daga kangi. Mun amfana matuka daga iliminsa, kwakwalwarsa gami da hazakarsa."

Daga karshe, Babangida ya roki Allah ya gafarta wa marigayi Ernest Shonekan yasa ya hutu.

Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa

A wani labari na daban, Chief Ernest Shonekan wanda ya jagoranci gwamnatin Najeriya ta rikon kwarya wanda gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta karba mulki daga hannunsa, ya rasu a sa'o'in farko na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

Shonekan ya rasu a wani asibitin Legas mai suna Evercare da ke Lekki yayin da ya ke da shekaru 85 sakamakon gajeriyar rashin lafiya, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Majiyoyi sun ce tsohon shugaban Najeriyar ya yi sama da wata biyu a asibiti kafin mutuwarsa daga bisani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel