Sama da yan ta'addan Boko Haram 8000 sun mika wuya, GOC

Sama da yan ta'addan Boko Haram 8000 sun mika wuya, GOC

  • Kwamandan Soji dake faggen fama ya bayyana adadin yan ta'addan da suka mika wuya kawo yanzu
  • Janar Eyitayo yace azabar da yan Boko Haram suke ji yasa suke mika wuya
  • Hukumar ta bada tabbacin cewa zata hukuntasu gaba daya

Maiduguri - Mukaddashin Kwamandan 7Div na hukumar Sojin Najeriya, Abdulwahab Eyitayo, ya bayyana cewa sama da yan ta'addan Boko Haram 8,000 suka mika wuya kawo yanzu.

Yace yan ta'addan sun fito daga mabuyarsu dake dajin Sambisa da kuma wasu mabuya.

Janar Eyitayo, wanda kuma shine Kwamandan Sector 1, Operation Hadin Kai, ya bayyana hakan ne yayin karban bakuncin Diraktan yada labaran hukumar, Onyema Nwachukwu, da wasu yan jaridar ranar Talata a Maiduguri, rahoton Ptimes.

Yace mika wuyan da yan ta'addan ke yi abu mai kyau ne kuma artabun da Soji kemusu ya kawo haka.

Kara karanta wannan

Fiye da 'yan Boko Haram 8,000 ne suka mika wuya tare da tuba, GOC

A cewarsa:

"Daya daga cikin dalilan da suke mika wuya haka shine wutan da Sojoji ke musu. Kuma dukkan kokarin namiji kawai yana yi ne don jin dadin iyalinsa, Shiyasa suke fito da iyalansu. Mun fara ganin alamu a watar Yuni."
"Mun yi ayyukan tare hanyar isar kayan abinci garesu, muna musu ruwan wuta, shi yasa."

Sama da yan ta'addan Boko Haram 8000 sun mika wuya, GOC
Sama da yan ta'addan Boko Haram 8000 sun mika wuya, GOC
Asali: Facebook

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

Tiyata Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa yan Najeriya da duniya cewa za'a hukunta yan Boko Haram da suka mika wuya, ba zasu tsira daga hukuncin laifukan da suka yi ba.

A hirar da yayi da manema labarai a hedkwatar rundunar dake Maiduguri, Janar Musa yace babu wanda zai yafewa dubban yan ta'addan Boko Haram da suka aikata muggan laifuka irin wannan, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

Yace lallai suna sane da maganganun da ake amma dokokin gidan Soja basu bada daman kashe mayakin da ya mika wuya ba.

A cewarsa, wajibi ne karramashi da kuma bashi wajen zama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel