Kashe min 'yaya biyar saboda Sheikh Zakzaky ba zai hana ni cigaba da binsa ba, Hajiya Jummai

Kashe min 'yaya biyar saboda Sheikh Zakzaky ba zai hana ni cigaba da binsa ba, Hajiya Jummai

  • Sheikh Ibrahim Zakzaky ya gayyaci ɗaukacin mabiyansa da suka tsira daga rikicin da ya faru da sojoji a Disamba 2015
  • Mutum biyu daga cikin wadanda suka rasa 'yayansu sun bayyana ra'ayoyinsu
  • Malamin ya rokesu su yi hakuri bisa abin da ya faru da su

Daya daga cikin wadanda suka rasa 'yan uwansu a rikicin da ya auku tsakanin Sojoji da daliban Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a 2015 ta bayyana irin rashin da tayi.

Makon nan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya gana da wadanda sukayi rashi a rikicin ranar 12 ga Disamba, 2015.

Hajiya Jummai Karofi wacce tace ta rasa 'yayanta biyar Bugu da kari jagoran mabiya mazhabar shi'a ya yi wa waɗanda suka samu halartar ganawar Nasiha da cewa kowace irin sadaukarwa ƙarama ce matukar kana kan gaskiya.

Kara karanta wannan

Sheikh Zazkazky Ya Gana da Mutanen da Suka Tsira da Rayuwarsu a Rikicin Mabiya Shi'a da Sojoji a 2015

"Ina son fadawa wadanda suka kashe min 'yaya cewa abinda suka yi min ba zai koreni daga wajen Sheikh Zakzaky da akidar Shi'a ba, shirye muke da mutuwa don kare addinin Musulunci."

Wani mutumi da yayi rashin 'yaya hudu lokacin, Isa Waziri Gwantu, ya lashi takobin cewa ba zasu taba fita daga mazhabar Sheikh Zakzaky ta Shi'a ba.

Kashe min 'yaya biyar saboda Sheikh Zakzaky ba zai hana ni cigaba da binsa ba Hajiya Jummai
Kashe min 'yaya biyar saboda Sheikh Zakzaky ba zai hana ni cigaba da binsa ba Hajiya Jummai
Asali: UGC

Zakzaky Ya Gana da Mutanen da Suka ya uwa Rikicin Mabiya Shi'a da Sojoji a 2015

Shugaban ƙungiyar mabiya shi'a (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya gana da mabiyansa da suka tsira da rayuwarsu a rikicin da ya faru tsakaninsu da sojoji a watan Disamba 2015.

Hakanan kuma Shehin malamin ya gana da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a rikicin.

Dailytrust ta rahoto cewa Zakzaky ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa iyalan ta'aziyya bisa rasuwar yan uwansu.

Kara karanta wannan

Jigon APC a Kano ya yi tir da tarbar da Buhari, APC suka yi wa Fani-Kayode a fadar Aso Villa

Malamin ya roke su da su tuna da irin matsanancin halin da jikan Manzon Allah (SAW), Imam Husaini, ya shiga a lokacin da aka kashe shi.

Bugu da kari jagoran mabiya mazhabar shi'a ya yi wa waɗanda suka samu halartar ganawar Nasiha da cewa kowace irin sadaukarwa ƙarama ce matukar kana kan gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng