An rufe dillaliyar da ta damfari ‘Dan wasan Man Utd, Cristiano Ronaldo a gidan kurkuku

An rufe dillaliyar da ta damfari ‘Dan wasan Man Utd, Cristiano Ronaldo a gidan kurkuku

  • Kotu ta samu matar da ake zargi da damfarar Cristiano Ronaldo da aikata laifi
  • An tabbatar da cewa Maria Silvia ta rika daukar kudi daga asusun ‘dan kwallon
  • Alkali ya yanke wa dillaliyar hukuncin dauri, amma ta yarda ta biya tarar kudi

Manchester, U.K - Wata dillaliya mai suna Maria Silvia ta damfari sabon ‘dan wasan gaban Manchester United, Cristiano Ronaldo wasu makudan kudi.

Jaridar Daily Star ta rahoto cewa wannan matar ta damfari Cristiano Ronaldo £250,000 (kusan Naira miliyan 140 a kudin Najeriya), bayan ya yarda da ita.

Rahotanni sun bayyana cewa tauraron ‘dan wasan ya damka wa Misis Maria Silvia katin bankinsa, wannan dillaliyar ta san lambobin sirrin asusunsa.

Ba a nan mummunan aikin wannan dillaliya ta tsaya ba, jaridar Punch ta rahoto cewa Silvia ta damfari dillalin Ronaldo, Jorge Mendes kudi har fam £14,000.

Kara karanta wannan

Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP

Maria Silvia ta taba yi wa Nani sata

Haka zalika ta damfari tsohon ‘dan wasan Manchester United, Nani, ta sace masa sama da fam £1,500.

A dalilin samun ta da wannan laifi tun a 2011, Alkalin ya yanke wa Maria Silvia mai shekara 53 a Duniya hukuncin daurin shekaru hudu a gidan gyaran hali.

Cristiano Ronaldo
Ronaldo a Manchester Utd Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kafin a shiga kotu a ranar Lahadi, wata kotun Portugal ta taba samun Silvia da laifi a shekarar 2017.

Sun Sports tace dillaliyar tayi ta facaka da makudan kudi tsakanin Fubrairun 2007 da Yulin 2010 bayan ta tafka sata daga asusun bankin ‘dan kwallon kafan.

Gaskiya ta fito bayan shekara da shekaru

Ronaldo ya kai karar Maria Silvia wajen ‘yan sanda a shekarar 2011. A wancan lokaci tauraron ya gabatar da takardun mu’amalar da aka yi a asusun bankinsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

Rahotanni sun ce sai a 2013 aka fara shari’a da dillaliyar, bayan lokaci ana ta zama a kotu, Alkali ya same ta da aikata laifin da ake zarginta a Satumban 2021.

An tabbatar da cewa Maria Silvia ta rika cire kudi daga asusun Ronaldo da sunan zai yi tafiya. Silvia ta yarda ta biya £7,680 domin guje wa zaman gidan yari.

Ronaldo ya dawo Ingila

A farkon Satumba aka ji cewa Kungiyar kwallon kafan Manchester United ta tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo zai sa riga mai lamba 7 ne a shekarar bana.

‘Dan wasan na kasar Portugal ya goya wannan riga a lokacin da ya buga wa Manchester United kwallo a karon farko tsakanin shekarar 2003 da kuma 2009.

Asali: Legit.ng

Online view pixel